YAN za ta gudanar da babban taro na ƙasa a Abuja

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kwamitin Amintattu na ƙungiyar Matasan Nijeriya (YAN) ya sanar da kafa Kwamitin Shirya Babban Taron ƙasa, tare da ba da umarnin fara shirye-shiryen gudanar da zaɓuɓɓuka a matakin jihohi da Babban Birnin Tarayya, Abuja.

A cikin wata sanarwar manema labarai da Kwamitin Amintattun ya fitar daga hedikwatar ƙungiyar da ke Abuja ranar 19 ga Yuli, 2026, ya bayyana cewa an kafa kwamitin ne bisa tanadin Sashe na 4, ƙaramin Sashe na 8 na Kundin Tsarin Mulkin YAN da aka yi wa kwaskwarima a shekarar 2024.

Sanarwar ta jaddada cewa Kwamitin Amintattu shi ne mafi girman sashi mai yanke hukunci a cikin ƙungiyar, kuma ya kafa kwamitin ne domin tabbatar da cewa babban taron ƙasa zai kasance mai gaskiya, haɗin kai da sahihanci.

Kwamitin ya ƙunshi wakilai daga shiyyoyin siyasar ƙasar nan guda shida, kamar haka:

Rt. Hon. Samuel Godstime Chukwubuikem – Shugaba, Rt. Hon. Comrade Shuaibu Sani – Sakatare, Rt. Hon. Famuyibo Nathaniel Oluwasegun – Mamba, Prince Mohammed Sani Hassan – Mamba, Amb. Muhammadu Bello Dabai – Mamba, Amb. Albert Ezenwata Nwangwu – Mamba, Amb. Henry Ejiroghene Oghwere – Mamba, Alh. Esinrogunjo Musbau – Mamba, Amb. Sen. Adeyelu Oluwadamilare Samuel – Mamba, Amb. Charles Ezeaniekwe – Mamba, Rt. Hon. Habiba Umar Iliyasu – Mamba.

Kwamitin Amintattun ya ɗora wa kwamitin nauyin tsara dukkan matakan da suka shafi babban taron ƙasa, ciki har da:

Gabatar da jigo, ranar gudanarwa, wurin taro da tsarin gudanar da babban taron.

Shirya cikakken kasafin kuɗi da dabarun tara kuɗaɗen gudanar da taron tare da haɗin gwiwar Babban Sakatariyar ƙungiyar da sauran masu ruwa da tsaki.

Kula da dukkan shirye-shiryen sufuri, masauki, tantance wakilai, tsaro, kafafen yaɗa labarai da walwalar mahalarta.

Jagorantar wayar da kai da tattara mahalarta daga rassan YAN na jihohi da sauran abokan hulɗa domin tabbatar da cikakken halarta.

Shirya ajandar taro, tattara rahotanni da tabbatar da adana dukkan bayanan taron.

Zama hanyar haɗin kai tsakanin Kwamitin Amintattu, shugabannin ƙasa, rassan jihohi da sauran abokan hulɗa kan dukkan batutuwan da suka shafi babban taron.

Kafa ƙananan kwamitoci tare da sa ido kan ayyukansu idan buƙata ta taso.

Tabbatar da cewa dukkan matakan gudanar da taron sun yi daidai da Kundin Tsarin Mulkin YAN na 2024, ƙa’idojin zaɓe da umarnin Kwamitin Amintattu.

Miƙa rahotannin ci gaban aiki lokaci-lokaci da kuma rahoton ƙarshe tare da shawarwari ga Kwamitin Amintattu cikin lokacin da aka tsara.

A wani mataki na shirye-shiryen babban taron, Kwamitin Amintattun ya umarci Mataimakin Kakakin Majalisar na ƙasa da ya yi aiki tare da Kakakin Majalisar na ƙasa wajen gaggauta naɗa Jami’an Gudanar da Zaɓe (Returning Officers) a jihohi 36 na tarayya da kuma Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Sanarwar ta ce, waɗannan jami’ai za su jagoranci tare da sa ido kan dukkan ayyukan zaɓe a matakin jihohi, bisa tanadin Kundin Tsarin Mulkin YAN da ƙa’idojin gudanar da zaɓe, kafin gudanar da Babban Taron ƙasa.

Kwamitin Amintattun ya bayyana cewa ana sa ran za a fara aiwatar da wannan tsari ba tare da ɓata lokaci ba domin bai wa jihohi damar kammala shirye-shiryensu.

A ƙarshe, Kwamitin ya buƙaci Kwamitin Shirya Babban Taron ƙasa, Mataimakin Kakakin Majalisar na ƙasa, mambobi, rassan jihohi da sauran masu ruwa da tsaki su yi aiki cikin gaskiya, ƙwazo da haɗin kai domin tabbatar da an gudanar da ingantaccen tsari da zai wakilci muradun matasan Nijeriya.

By ukarofi

Leave a Reply