Tafiya da kowa a gwamnati har yanzu na fama da ƙalubale – Halima Mahdi

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe

Wata mai rajin tabbatar da daidaito da tafiya da kowa a harkokin shugabanci, Hajiya Halima Mahdi, ta ce duk da yawaitar kira da wayar da kai kan muhimmancin tafiya da kowa (inclusiveness), har yanzu mata, matasa da masu nakasa ba sa samun isasshen wakilci a gwamnati da wuraren yanke manyan hukunci.

Halima Mahdi, ta bayyana haka ne a wata hira, inda ta ce ana yawan jin gwamnati da hukumomi suna magana kan tafiya da kowa, amma hakan bai bayyana sosai ba a naɗe-naɗen muƙamai, tsara manufofi da aiwatar da shirye-shiryen gwamnati.

Ta ce ainihin manufar tafiya da kowa ita ce tabbatar da cewa kowane rukuni na al’umma ya samu damar bayar da gudunmawa wajen tafiyar da gwamnati ba tare da la’akari da jinsi, shekaru ko nakasa ba.

A cewarta, ci gaba da ware mata, matasa da masu nakasa daga manyan muƙaman gwamnati na hana al’umma cin gajiyar basira da ƙwarewar da waɗannan rukunai suke da ita.

Ta ƙara da cewa ba za a samu ci gaba mai ɗorewa da kyakkyawan shugabanci ba sai an samar da dama iri ɗaya ga kowa tare da tabbatar da adalci wajen naɗe-naɗe da yanke hukunci.

Don haka ta buƙaci shugabannin siyasa da masu tsara manufofi su wuce matakin furuci kawai, su aiwatar da manufofin da za su tabbatar da wakilci na gaskiya ga mata, matasa da masu nakasa.

Haka kuma ta yi kira ga hukumomin gwamnati da su kawar da duk wani cikas da ke hana wasu rukunin al’umma samun damar shiga harkokin shugabanci, tana mai cewa auna nasarar tafiya da kowa ya kamata ya kasance bisa abin da ake aiwatarwa, ba kalaman da ake yi ba.

Ta jaddada cewa gina al’umma mai adalci da ci gaba na buƙatar a tabbatar da cewa babu wani rukuni da aka bari a baya, tare da bai wa kowa damar taka rawa wajen ci gaban ƙasa.

By ukarofi

Leave a Reply