Daga JAMIL GULMA a Kebbi
A cikin shirin sa na tallafi ga marayu da manoma masu ƙaramin ƙarfi Honarabul Sani Yakubu Ƴargiwa ya raba abinci da takin zamani da motocin noma.
Honarabul Sani Yakubu ya bayyana cewa waɗannan kayan dama ba nasa ba ne na al’umma ne saboda haka ya karɓo kuma ya isar da waƙilci kamar yadda aka tura shi.
Ya ƙara da cewa wannan ba zai isa ga kowa ba amma dai mutane kowa ya yi haƙuri da abinda ya samu saboda duk wanda ke bibiyar harkokin majalisun tarayya yana sane da cewa tun kasafin shekarar 2025 da ta gabata ba a saka masa hannu ba ballantana na wannan shekara.
Ya ƙara da cewa bayan wannan kuma nan gaba kaɗan za a gudanar da auren marayu 200 wanda ya ke shiryawa lokaci zuwa lokaci wanda yanzu haka shirye-shirye ya yi nisa.
Daga cikin kayan da aka raba akwai buhun takin zamani 330 ga manoma, buhunan abinci daban-daban 330 ga marayu, motocin noma na hannu (Power Tiller), Injinan chasar shinkafa.
