Matakin EFCC na rufe asusun gwamnatin Osun na bisa doka, inji Falana

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Lauyan kare haƙƙin ɗan-adam kuma Babban Lauyan Nijeriya (SAN), Femi Falana, ya kare matakin Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati EFCC, inda ya ce ta yi aiki ne bisa ikon da doka ta ba ta a lokacin da ta sanya wa asusun gwamnatin Jihar Osun takunkumi.

Falana ya bayyana haka ne a wata hira da gidan talabijin na Channels a ranar Juma’a a shirin ‘Politics Today’, a inda ya ce hukumar ba ta yi wani abu da ya saɓa wa doka ba, kuma Shugaba Bola Tinubu ma yana sane da halascin matakin na EFCC a lokacin da ya koka kan lokacin da aka aiwatar da shi.

A cewar babban lauyan, dokar ƙasa ta ba wa EFCC ikon rufe asusun gwamnatocin tarayya, na jihohi ko na ƙananan hukumomi muddin aka samu buƙatar yin hakan, sannan matuƙar ta tuntuɓi kotu acikin sa’o’i 72.

Falana ya kuma ƙalubalanci masu sukar hukumomin yaƙi da rashawa kan su daina bincike saboda zaɓuka suna kusantowa, yana mai cewa barin hakan barazana ce ga tattalin arziƙin ƙasa.

Game da tsoma bakin shugaban ƙasar, Femi Falana ya ce batun lokacin da aka aiwatar da hukuncin abu ne da ya dace a ce Antoni Janar na Ƙasa ne ya ji da shi.

Wannan cece-kuce ta samo asali ne a ranar Laraba, a lokacin da Gwamnan Osun, Ademola Adeleke ya zargi EFCC da rufe ɗaya daga cikin asusun gwamnatin jihar, yana mai bayyana hakan a matsayin abin da aka siyasantar, musamman ganin yadda hakan ya zo kusa da zaɓen gwamnan jihar.

Daga bisani a washegarin ranar ne Shugaba Bola Tinubu ya umarci hukumar da ta gaggauta buɗewa, bisa la’akari da lokacin da ta ɗauki matakin nata.

By Babaji