
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙoƙarin Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna na inganta harkar lafiya a Kaduna ya samu ƙarin ƙarfi, bayan Majalisar Kasashen Musulmi ta Muslim World League (MWL) ta kammala gina wata katafariyar cibiyar kula da cututtukan zuciya ta zamani a yankin Tudun Wadada ke Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Kudu.
Za a ƙaddamar da cibiyar ne a ranar Talata, 11 ga Agusta, 2026, a yayin wani biki da Sakatare Janar na majalisar ta Muslim World League, Sheikh Mohammed Bin Abdulkarim Al-Issa zai jagoranta.
Rahotanni sun bayyana cewa, cibiyar za ta samar da gwaje-gwaje, magani da kulawa ta zamani ga masu fama da cututtukan zuciya, tare da kula da marasa lafiya ba tare da la’akari da addininsu ba.
Gwamnatin Kaduna ta ce cibiyar za ta taimaka wajen rage yawan mutanen da ke zuwa ƙasashen waje neman maganin cututtukan zuciya.
Hakan na zuwa ne bayan gwamnatin jihar ta ce ta inganta cibiyoyin lafiya guda 255 na matakin farko, tare da ƙara kayan aiki da ma’aikatan lafiya a faɗin jihar.
