Badaƙalar hukumar bogi: ICPC ta shawarci a hukunta jami’an gwamnati 13

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ICPC, ta bayar da shawara ga Gwamnatin Tarayya kan a hukunta wasu jami’an gwamnati guda 13 bisa rawa da suka taka a badaƙalar haramtacciyar hukumar nan da aka kira da Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC).

Hakan na ƙunshe ne a cikin rahoton binciken yadda, hukumar, wadda ba ta samu amincewa ba a dokance, ta samu damarmaki kan gudanar da harkokinta a ofisoshin gwamnati, tsare-tsaren kuɗaɗe da wasu damarmakin gudanarwa.

Haka kuma, ICPC ta bada shawarar a gurfanar da Adeniyi Adeyemi, wanda ya gabatar da kansa a matsayin darakta-janar na PFIPC bisa ayyukan bogi, sojan gona, yin kalaman ƙarya akan jami’an gwamnati da gabatar da kalaman yaudara. Waɗannan shawarwari sun nuna sabuwar alama kan yadda hukumar bogin ta kutsa cikin ikon gwamnatin tarayya kafin Fadar Shugaban Ƙasa ta nesanta kanta da ita.

Wannan bincike dai ya biyo bayan umarnin da Shugaba Bola Tinubu ya bai wa ICPC na ta gudanar da bincike kan PFIPC da kuma bayar da rahoto a kai. A rahoton farko da hukumar yaƙi da rashawan ta fitar a ranar 6 ga Agusta, ICPC ta ce Gwamnatin Tarayya ba ta taɓa naɗa Mista Adeyemi ba a wani aiki kuma babu wata doka ko cibiyar gwamnati da ta samar da PFIPC.

A yanzu kuma, ICPC ta bayar da shawarwar a ɗauki matakin hukunta Mimi Abu, daraktar shirya tsare-tsare da ci-gaba a Ma’aikatar Ma’aikatan Tarayya; Rosemary Achem, mai taimakawa kan harkar gudanarwa na Darakta-Janar na Ofishin Kasafi na Tarayya; da Patricia Akhigbe, mataimakiyar darakta a Ma’aikatar Kasafi da Shirye-shiryen Ƙasa.

Sauran sune Aminu Abdullahi, jami’in jaddawalim ayyuka na Ofishin Rabawa a Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya; Bello Abdullahi, Mataimakin IPSAS, na Reshen kula da Asusun Ƙasa na Ofishin Akanta Janar na Ƙasa; Sanni Olubunmi, darakta a reshen Sanya Ido na OAGF; da kuma Jousha Kadiri Luka, darakta a Reshen Haɗakar Asusun Ƙasa na OAGF.

Jaddawalin sunayen ya kuma ƙunshi Muazu Balami, mataimakin darakta a Reshen Haɗari, Nazari da Sanya Ido na OAGF; Omameh Florence, mataimakiyar darakta a Reshen Sanya Ido a OAGF; Akinlose Moses, Reshen Sany Ido na OAGF; Ogaba Harry, babban akanta a OAGF; Esther Orji Okoli, babbar jami’a mai daraja ta I a OAGF; da kuma Ogunbade Habeebat Ajibola, manaja a Reshen Biyayya da Gudanarwa na Hukumar kula da Ci-gaban Fasahar Sadarwa ta Ƙasa (NITDA).

Kazalika, ICPC ta bai wa cibiyoyin da al’amarin ya shafa waɗansu shawarwari na ɗaukar matakan gyara da ta sanya acikin rahoton nata.

By Babaji

Leave a Reply