Tinubu ya shigar da ƙarar daƙile fitar da rahoton Amurka da aka danganta da zargin safarar ƙwayoyi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya shigar ƙarar ƙalubalantar wata kotun Amurka, inda ya nemi a dakatar da Ma’aikatar Shari’ar ƙasar, Cibiyar Bincikenta (FBI) da Hukumar Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi (DEA) daga fitar da rahotanni da ke zargin alaƙanta safarar ƙwayoyi da aka sanya shi a matsayin ɗaya daga cikin masu hannu a ciki.

Rahotanni sun bayyana cewa, wani Ba’amurken ɗan gwagwarmayar ƙoƙarin tabbatar da gaskiya da adalci mai suna Aaron Greenspan ne ya tono rahotannin, inda ya kuma shigar da ƙarar neman aiwatar da ‘yancin samun labari akan hukumomin Amurka da dama na neman a fitar da takardu da suke alaƙanta bincike da ya haɗa da Shugaba Tinubu.

Daga cikin buƙatun da Greenspan ya gabatar akwai neman FBI ta fitar da baki ɗaya kundin rahoton bincikenta akan Tinubu, da kuma takardun hira guda 302 da suke da dangantaka da batun a lokacin tsakanin 1992 da 1993.

Shari’ar ta kuma ƙunshi zargin wani rahoto da aka fitar a 1993 na ƙwace wasu kadarori a Amurka da suka kai darajar Dala 460,000 da aka alaƙanta su da shugaban Nijeriyar.

A cewar wani kundin kotu mai shafi 16 da Lauyan Tinubu da tawagar shari’arsa – Christopher W. Carmichael, Victor P. Henderson da Oluwole O. Afolabi suka aike wa gidan talabijin na Channels a ranar Asabar, Shugaban ya ce fitar da rahotannin ka iya tauye masa ‘yancin ɓoye sirri. Tawagar shari’ar ta ce bayanin da aka gabatar kan ƙwace kadarorin bai bayyana cewa ko akwai binciken babban laifi ba ko akasin haka da ya haɗa da shugaban ƙasar.

Haka kuma, lauyoyin nasa sun ce abin da ƙorafin Greenspan ke nema shi ne bayanan da ba a riga an bayyana su ba ne a fili, inda suka ce saboda haka ne suka buƙaci Kotun Ƙoli da ta duba maslahar sirri wajen cigaba ba ɓoye bayanin, wanda da za a fitar da shi tun a baya.

Akan haka ne lauyoyin suka kuma nemi kotun da kada ta ba wa Greenspan damar samun kundin bayanan, waɗanda aka ƙi fitar da su ga al’umma bisa dalilan shari’a.

By Babaji

Leave a Reply