Bankuna ne suka kai kashi 92 na rahoton haramtaccen hada-hadar kuɗi a 2025 — NFIU

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Bankunan ajiyar kuɗi na Nijeriya sun gabatar da kusan kashi 92 cikin 100 na rahotannin hada-hadar kuɗi da ake zargi da aikata laifi da Hukumar Leƙen Asirin Kuɗi ta Nijeriya (NFIU) ta karɓa a shekarar 2025, duk da cewa adadin irin waɗannan rahotanni ya ragu sosai idan aka kwatanta da shekarar 2024.

Hakan na ƙunshe cikin rahoton shekara-shekara na NFIU na 2025, wanda ya nuna cewa hukumomi da cibiyoyin da doka ta wajabta musu kai rahoton hada-hadar kuɗi sun gabatar da rahotannin Hada-hadar Kuɗaɗe Da Ake Zargi (STR) guda 42,082 a cikin shekarar.

Daga cikin wannan adadi, bankunan ajiyar kuɗi sun gabatar da rahotanni 38,715, yayin da sauran cibiyoyin kuɗi suka gabatar da 2,185. Kamfanoni da sana’o’in da ba na kuɗi ba amma doka ta sanya su cikin masu bayar da rahoto sun gabatar da 1,029.

Masu gudanar da harkokin kasuwar hannayen jari da kamfanonin inshora sun gabatar da rahotanni 104, yayin da masu ba da sabis na kadarorin dijital, ciki har da harkokin da suka shafi kuɗaɗen intanet na cryptocurrency, suka kai rahotanni 49.

Baya ga rahotannin STR, NFIU ta ce ta karɓi Rahotannin Ayyukan da ake Zargi (SARs) guda 10,513 da kuma sama da Rahotannin Hada-hadar Kuɗi (CTRs) miliyan 41.7 a shekarar 2025. Bankuna su ma sun fi sauran cibiyoyi yawan gabatar da rahoton SAR, inda suka kai guda 8,313. Sauran cibiyoyin kuɗi sun gabatar da 1,816, yayin da kamfanonin kasuwar hannayen jari da inshora suka kai 295. Masu ba da sabis na kadarorin dijital kuwa sun gabatar da 89.

Rahoton ya nuna cewa bankunan ajiyar kuɗi sun gabatar da CTR sama da miliyan 37.2, wanda ya kai kusan kashi 89.2 cikin 100 na jimillar rahotannin. Sauran cibiyoyin kuɗi sun kai miliyan 4.21, yayin da masu gudanar da kasuwar hannayen jari da kamfanonin inshora suka gabatar da 289,296.

NFIU ta bayyana cewa tsarin bayar da rahotannin ya shafi hada-hadar kuɗi da ta kai wani matakin da doka ta ƙayyade, hada-hadar da ake zargi da kuma ayyukan da ake ganin suna da alamun laifi. Haka kuma, tsarin ya shafi rahotannin da suka shafi yaƙi da safarar kuɗaɗen haram, da kuma tallafa wa ta’addanci da yaɗa makamai masu linzami.

Hukumar ta ce tana aiki tare da wasu hukumomin sa ido, ciki har da Babban Bankin Nijeriya (CBN), Hukumar Kula da Inshora ta Nijeriya (NAICOM), Hukumar Kula da Kasuwar Hannayen Jari (SEC) da Sashen Musamman na Kula da Safarar Kuɗaɗen Haram (SCUML) domin tabbatar da cewa cibiyoyin da doka ta wajabta musu bayar da rahoto suna bin ƙa’idojin da aka shimfiɗa. Rahoton NFIU ya nuna cewa adadin STR da bankuna suka gabatar ya ƙaru a hankali a dukkanin sassan shekarar 2025.

A zangon farko na shekarar, bankuna sun gabatar da rahotanni 9,134. Wannan adadi ya koma 9,658 a zangon biyu, sannan ya kai 9,891 a zangon uku, kafin ya ƙaru zuwa 10,032 a zangon huɗu. Sai dai duk da wannan ƙaruwa a rahotannin da bankuna suka gabatar, jimillar rahotannin STR da NFIU ta karɓa daga dukkan masu bayar da rahoto ta ragu matuƙa idan aka kwatanta da shekarar 2024.

A shekarar 2024, hukumar ta karɓi rahotannin STR guda 82,143, amma adadin ya koma 42,082 a 2025, abin da ke nuna raguwar kusan kashi 48.8 cikin 100. Haka kuma, rahotannin SAR sun ragu da kusan kashi 55 cikin 100, daga 23,364 a 2024 zuwa 10,513 a 2025.

By ukarofi

Leave a Reply