‘Yan sanda sun kama wani mutum ɗauke da abincin yara masu cutar Tamuwa guda 1500 a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

‘Yan sanda sun kama wani mutum mai suna Muhammad Aliyu a ƙaramar hukumar Batagarwa a lokacin da yake ƙoƙarin karkatar da abincin ƙananan yara masu ɗauke da cutar Tamuwa wanda ake kira da suna yar ƙwamaso.

Kamar yadda jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda a Katsina sun sami nasarar kama wanda ake zargi yana ƙoƙarin karkatar da abincin yara( RUTF) mai suna yar ƙwamaso.

Waɗannan kayan abinci a samar da su domin rabawa kyauta a cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko a faɗin jihar.

Bincike na farko da ya gudanar kamar yadda DSP Abubakar Sadiq yace wanda ake zargi ya faɗawa ‘yan sanda cewa ya saya a hannun zaharaddin Musa Malami n kiwon lafiya wanda ake nema ruwa a Jallo.

A halin yanzu wanda ake zargi yana hannun yan sanda yana taimakawa wajan gano da kama abokan hulɗar wajen karkatar da Waɗannan kayan jinƙai.

Yan sanda sun gargaɗi mutane da su guji ajiye,saidawa ko karkatar da RURF da sauran kayan kiwon lafiya.

“RUTF ba na saidawa bane,duk wanda aka samu yana tare da wannan kayan ƙwamaso doka za ta yi halin ta.

Kwamishinan ‘yan sanda CP Ali Umar Fage ya bada umurni a yi cikakken bincike daga nan a gurfanar da shi a gabanin kotu.

By ukarofi

Leave a Reply