Yanzu-yanzu: Majalisar Wakilai ta bankaɗo hukumomin bogi 12, asusun banki 58 da ma’aikata 39 da aka danganta da Adeyemi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kwamitin wucin-gadi na Majalisar Wakilai kan binciken badaƙalar zargin kafa hukumar nan ta PFIPC da aka kira da ta bogi, ya ayyana cewa ba a samar da wata hukuma ba mai wannan sunan a dokance, inda ya bayyana ta a matsayin hukumar gwamnati ta bogi.

A binciken da kwamitin ya fitar a ranar Laraba, ya ce takardar naɗa muƙami da Adeyemi Adeniyi ya gabatar ita ma ta bogi ce, yayin da ta kuma bankaɗo asusun banki guda 58 da ma’aikata 39 da aka danganta da shi Adeyemi da aka kira da darakta-janar na PFIPC.

Kwamitin ya ce, binciken nasa hallau, ya tsame hannun Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila daga dukkan wani abin da ya shafi hukumar da Shugaban kwamitin, sannan Hon. Ibrahim Sani Madaki ya yaba wa Gbajabiamila bisa ankarar da hukumomi game da wanzuwa da ayyukanta. Madaki ya bayyana cewa, shigar Gbajabiamila cikin al’amarin ya taimaka wa abin da kwamitin ya kira da “taron cibiyoyin bogi da ke dodorido a matsayin hukumomin gwamnati”.

Kwamitin a yayin zaman nasa na ranar Larabar, ya bayyana cewa bayanan kuɗi ya nuna cewa sama da asusu 30 cikin 58 ɗin suna aiki ne da sunan hukumomi guda tara, kamfanoni, gidauniyoyi ko kuma ofisoshi masu kama da su.

Haka kuma, kwamitin, wanda Hon Yusuf Gagdi yake jagoranta, ya ce an haɗa asusun da lambar tantancewa ta banki (BVN) da wasu bayanai da suke da alaƙa da Frins Adeniyi Adeyemi, da kuma Adeyemi Matthew a wasu kundaddakin bayanai. Saidai, ya ce bai tabbatar ko dukkanin asusun da hada-hadar da aka gudanar acikinsu haramtattu ba ne, yana mai cewa yana cigaba da duba rahotannin rajista, sahihancin asusu, bayanan mallaka, sahalewa da rahoton hada-hada.

A cewar hukumar, kimanin mutane 39 aka gurfanar ko aka ayyana su a matsayin ma’aikatan hukumar da suka haɗa da ƙanana, matsakaita da manyan jami’ai. Sannan, yana bincike kan yadda aka ɗauki ma’aikatan aiki, ba su takardun ɗaukar aiki da ba su katin shaida (IDcard). Sauran ababen sun haɗa da yadda ake biyan su albashi, alawus da kuma iƙirarin cewa an nemi wasu su biya kuɗi kafin a ba su aiki.

Kazalika, kwamitin ya ce ya bankaɗo ƙarin wasu hukumomi guda 12 da ake zargin suna aiki a matsayin cibiyoyin gwamnati, waɗanda suke da alaƙa da Adeyemi.

Ga jaddawalin sunayen hukumomin kamar yadda kwamitin ya gabatar: “…the Confederation of United Nations Youths, FCT Investment Promotion Agency and Public-Private Partnership, FCT Investment Promotion Council and Public-Private Partnership, Foreign Investment Promotion Agency, United Nations Youth Global Agency, United Nations Youth Global Foundation, World United Nations Youth Global Foundation, World Entrepreneurship University Limited, World Enterprise University Limited, FCT Investment Promotion Act, FCT Promotion Agency and Olubadan of Ibadan Foundation.”

A ƙarshe, kwamitin ya ce yana cigaba da gudanar da bincike, sannan za a fitar da shawarwari daga binciken nasa kan zargin PFIPC da sauran cibiyoyin da aka bankaɗo.

By Babaji