Al’ummar Dutsen Safe sun koka kan lalacewar hanyar zuwa kasuwar ’Yarkutungu a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Mazauna unguwar Dutsen Safe a ƙaramar hukumar Katsina sun yi kira ga Gwamna Dikko Raɗɗa da gyara hanyar Dutsen Safe zuwa kasuwar Yar kutungu wanda yake kawo babbar matsala wajen shiga da fita da kayan masarufi a yankin.

Sunce hanyar da ta haɗe al’ummomi da sannaniyar kasuwar Yar Kutungu a shekara da dama ya yi lalacewar da masu ababen hawa, ‘yan kasuwa da al’ummar yankin matsalar kai wa da komawa a wannan hanyar.

Wani mazaunin garin Babangida Abba ya shaida cewa wannan hanyar ya yi shekara da shekaru cikin mummunar hali da ta sanya lalacewar ababen hawa da yadda ‘yan kasuwa suke tafka asarar kayan masarufi.

“Sunyi kira ga Gwamna Dikko Raɗɗa da ya sanya aikin hanyar cikin tsarin gina hanyoyi a birane.

Na kai shekara 20 da zaman a unguwar Dutsen Safe,tun a lokacin zuwa yanzu hanyar ta kasanci abin damuwa ga al’ummar yankin don haka nake kira ga Gwamna Dikko Raɗɗa ya kawo mana ɗauki,”Inji Abba.

“Gwamna Raɗɗa mai sauraren jama’a ne,ina mai imani za sanya aiki hanyar ƙarkashin shirin gyara birane,”Abba ya ce.

Wata mata mai zaune a yankin Fatima Khalid tace ana samun matsala musamman lokacin damina,ta bayyana cewa mazauna unguwar su kan faɗa cikin wahala wajen kaiwa da komowa.

Khalid wanda take saida kayan yara a kasuwar yar kutungu,ta nuna cewa lalacewar hanyar ta ba miyagun mutane dama na kai hare hare ga matafiya a kan hanyar.

Shima James Chuku ya bayyana cewa a duk lokacin da aka sami ruwan sama ‘yan kasuwa na shiga damuwa yadda za su fidda kayan su zuwa kasuwa.

By ukarofi

Leave a Reply