UNICEF ta buƙaci manema labarai su matsawa gwamnati kan kasafin yara

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe

Asusun tallafawa yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ya bukaci manema labarai su matsa wa gwamnatoci lamba wajen ƙara kuɗaɗen da ake warewa yara tare da bibiyar yadda ake sakin da kuma kashe kuɗaɗen domin tabbatar da cewa sun haifar da ingantattun ayyuka.

UNICEF ta ce duk da cewa yara masu shekaru daga haihuwa zuwa shekara 18 sun fi rabin al’ummar ƙasar, ana ci gaba da samun giɓi wajen ba su fifiko a kasafin kuɗin gwamnati.

Shugabar ofishin UNICEF na Bauchi, Nuzhat Rafique, ce ta yi wannan kira a Bauchi, yayin wani taron tattaunawa da manema labarai kan samar da kuɗaɗen gwamnati ga yara.

Taron, wanda ma’aikatar kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki da huldar ɓangarori da dama ta Jihar Bauchi ta shirya tare da haɗin gwiwar ofishin UNICEF na Bauchi, ya samu halartar ‘yan jarida daga Bauchi, Gombe da Filato.

Rafique, wadda ƙwararren jami’in UNICEF kan Ilimi, Abdulrahman Ado, ya wakilta, ta ce kafafen yaɗa labarai na da muhimmiyar rawa wajen neman ingantaccen kasafi, sakin kuɗaɗe a kan lokaci da kuma ganin an samu sakamako mai ma’ana ga yara da mata.

Ta buƙaci ‘yan jarida su rika tambayar ‘yan takarar siyasa kan shirye-shiryensu na magance matsalolin da ke addabar yara da mata, musamman yayin da zaɓen siyasa ke ƙara ƙaratowa.

“Mata da yara na fuskantar ƙalubale da dama. Yara da yawa ba sa zuwa makaranta, akwai matsalar tamowa, rashin ingantattun cibiyoyin kiwon lafiya da ƙarancin ruwa da tsaftar muhalli, da sauran ƙalubale,” in ji ta.

Ta ce ya kamata manema labarai su tabbatar da cewa ‘yan siyasa sun bayyana tsare-tsaren da suke da su na magance waɗannan matsaloli tare da tambayar su yadda za su samar da kuɗaɗen aiwatar da alƙawurran.

Shi ma ƙwararren UNICEF kan manufofin zamantakewa, Yusuf Auta, ya ce ya kamata a bai wa yara fifiko tun daga matakin tsara kasafi har zuwa aiwatar da shi.

Auta ya ce yara masu shekaru daga haihuwa zuwa 18 sun ƙunshi sama da kashi 51 cikin 100 na al’ummar ƙasar, amma duk da haka, kasafin gwamnati na yawan karkata ne ga buƙatun manya.

“Abin takaici, kasafi ya fi karkata ga manya maimakon yara masu shekaru 0 zuwa 18, wadanda suka ƙunshi sama da kashi 51 cikin 100 na al’umma,” in ji shi.

Ya buƙaci ‘yan jarida su daina tsaya wa kan rahoton adadin kuɗin da aka ware kawai, su riƙa bibiyar ko an saki kuɗaɗen, yadda aka kashe su da kuma irin sakamakon da aka samu.

“Bayan an ware kuɗaɗe a kasafi, nawa aka saki? Bayan an kashe kuɗaɗen, wane sakamako aka samu? A nan ne ake auna hakikanin ci gaba,” in ji Auta.

Ya ce kafafen yaɗa labarai na da damar yin amfani da matsayinsu na masu sa ido wajen riƙe gwamnatoci da alhakin yadda suke kashe kuɗaɗen da aka ware wa yara.

A cewarsa, bai isa gwamnati ta ware biliyoyin naira ga harkokin yara ba tare da an tabbatar da cewa kuɗaɗen sun sauya rayuwar yaran da ake nufi da su ba.

“Sakamako shi ne abu mafi muhimmanci. Bayan an ware biliyoyi da tiriliyoyin naira a kasafin kudi, kafafen yaɗa labarai suna da rawar da za su taka wajen sauya labari ta hanyar riƙe gwamnati da alhakin kashe kuɗaɗen,” in ji shi.

By ukarofi

Leave a Reply