
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ministan Ilimi, Dakta Maruf Tunji Alausa, ya bayyana cewa suna zargin an siyar da tambayoyin jarrabawar NECO akan Naira 3,000 gabanin ainihin lokacin rubuta ta, yayin bayyana matakin satar amsar jarrabawa a Nijeriya.
Alausa ya faɗi haka ne a ranar Alhamis, a wani zama da ya ƙunshi tawagar Ƙungiyar Masu Makarantu Masu Zaman kansu ta Ƙasa (NAPPS) da wasu masu ruwa da tsaki a fannin ilimi, inda ya gargaɗi iyaye, malamai, masu makarantu, shugabannin makarantu, masu sanya ido da ɗalibai akan ayyukan da ka iya tauye darajar jarrabawar da ake shirya wa ɗalibai.
Ministan ya bayyana cewa satar amsar jarrabawar ya zama abin damuwa a ‘yan shekarun nan, lamarin da ke haifar da koma-baya ga ɗaliban da suke shiryawa tsaf domin jarrabawa daga masu samun satar amsa.
Ministan ya ƙara da cewa, haɗarin yanzu ya wuce ha’intar sakamakon jarrabawa inda ya yi gargaɗin yawaitar satar amsa ka iya gurɓata tunanin ɗalibai masu nagarta wajen bin salon masu satar amsa domin gogayya da su wajen samun maki. Ya tunatar da wani hali da aka yi zargin cewa ana siyar da tambayoyin jarrabawa akan Naira N3,000.
A nata jawabin, Ƙaramar Ministar Ilimi, Farfesa Suwaiba Sa’id Ahmad, ta yi kira ga masu makarantu da su bai wa gyare-gyaren ma’aikatar goyon baya, tana mai cewa daidaita tambayoyin jarrabawa za su taimaka wajen ƙarfafa matakin tsaro ga tambayoyin jarrabawa tare da kauce wa yoyonsu. Ta bayyana cewa, muddin aka ƙarfafa matakin kulawa, hakan zai taimaka wa ɗalibai wajen ƙara himma kan mayar da hankali ga shirya wa jarrabawa tare da ƙaurace wa ƙoƙarin satar amsa.
Kazalika, ta roƙi makarantu da su kammala tsara jaddawalin harkokinsu da kira ga mayar da hankali kan karatu, tana mai tabbatar wa masu ruwa da tsaki cewa ma’aikatar za ta cigaba da damawa da su yayin aiwatar da gyare-gyaren da ma’aikatar ta sanya a gaba a fannin ilimi.
