Makusanta sun nuna gamsuwa da naɗa ƙadiri sarautar Oshi-Ozoya a Kano

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

’Yan uwa da abokan arziki sun nuna gamsuwa tare da bayyana farin cikinsu kan naɗa Muhammad Abdulkadir, FCA, sarautar Oshi-Ozoya na al’ummar Edo mazauna Jihar Kano.

An bayyana hakan ne yayin wani taron taya shi murnar samun wannan sarauta da aka gudanar a wani ɗakin taro da ke kan Lodge Road a Kano.

Da take jawabi a wajen taron, Asiya Balaraba Abdullahi Umar Ganduje ta bayyana Kano a matsayin gida ga duk wani ɗan Nijeriya mai son zaman lafiya da bin doka da oda.

Ta ce Muhammad Abdulkadir mutum ne da ya kasance yana bayar da gudunmawa wajen ci gaban al’ummarsa da kuma Jihar Kano baki ɗaya.

Wasu daga cikin ’yan uwa da abokan arziki da suka gabatar da jawabai a wajen taron sun haɗa da Malam Aminu Kadiri, Alhaji Muhammad Egemiyar Magemi, Alhaji Jamilu Abdullahi Dahur, shugaban horar da masana ƙididdigar kuɗi na Kano a ICAN, da kuma Hon. Eminofi Yunusa, tsohon shugaban ma’aikata a Ofishin Mataimakin Gwamnan Jihar Edo.

Sauran mahalarta taron ma sun bayyana gamsuwa da wannan naɗi, suna masu fatan sabon mai sarautar zai yi amfani da matsayin wajen ci gaba da hidimtawa al’ummar Edo da sauran jama’ar Kano.

Da yake nasa jawabin, sabon Oshi-Ozoya, Muhammad Abdulkadir, ya bayyana godiyarsa ga Sarkin al’ummar Edo mazauna Kano bisa karrama shi da wannan sarauta.

Ya ce wannan naɗi zai ƙara masa ƙwarin gwiwa wajen ci gaba da bayar da gudunmawa ga al’ummar Edo da kuma Jihar Kano baki ɗaya.

Muhammad Abdulkadir ya bayyana al’ummar Kano a matsayin masu karamci da son zaman lafiya, tare da jaddada cewa jihar ta kasance wurin da ba a nuna bambanci tsakanin jama’a.

Ya kuma yaba wa Masarautar Kano ƙarƙashin jagorancin Khalifa Malam Muhammadu Sanusi II da kuma Gwamnatin Jihar Kano bisa ƙoƙarin da suke yi na tabbatar da tsaro da zaman lafiya a jihar.

By ukarofi