Ku daina raba babura a matsayin tallafi – Gargaɗin Ministan Tsaro ga gwamnoni

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya yi kira ga gwamnoni da su daina bayar da kyautar babura a matsayin tallafi ga al’umma, yana mai gargaɗin hakan a wasu lokutan na shiga hannun ‘yan bindiga waɗanda suke amfani da su wajen aikata miyagun ayyukansu.

Janar Musa ya bayyana haka ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels a ranar Alhamis, inda ya kuma ce Nijeriya ta samu wasu nasarori a fannin tsaro a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, sakamakon samun sauƙin ƙaddamar da hare-hare a sassanta.

Ya ce, babura musamman masu tsada, suna bai wa ‘yan ta’adda dama saboda ana iya zirga-zirga da su ta hanyoyi masu wahalar tafiya, shiga ƙauyuka da tserewa cikin sauƙi kafin jami’an tsaro su kawo ɗauki. Don haka ya kirayi gwamnoni da su sake nazari kan matakansu na raba babura a matsayin tallafi. “Ko da sai kun bayar, ku ba su masu sauƙin farashi ta yadda ba za a iya amfani da su ba wajen aikata miyagun laifuka”, inji shi.

Ministan ya kuma yi kira ga mahukunta da su gano tare da sanya ido kan kasuwannin da ire-iren waɗannan babura da ake aikata ta’addanci da su suke zagayawa domi daƙile hanyoyin isar da su zuwa ga ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda.

Ya bayyana cewa, hukumomin tsaro sun gano haramtattun kasuwanni da tashoshin mota da ‘yan ta’adda suke amfani da su wajen safarar bindigu da alburusai zuwa yankunan da suke aiwatar da miyagun ayyukansu, yana mai cewa sanya ido a guraren na haifar wa ƙungiyoyin ta’adda tsaiko wajen gudanar da ayyukansu.

Ministan ya ƙara da cewa an samu ingancin tsaro a Nijeriya, inda a yanzu hare-haren Boko Haram da ISWAP sun yi sauƙi ba kamar yadda aka saba gani ba a baya. Kazalika, tsohon Babban Hafsan Tsaron ƙasar ya ce a yanzu sojoji na kai wa ‘yan ta’adda hare-hare a maɓoyarsu tare da ceto mutanen da aka yi garkuwa da su da ƙwato makamai, yana mai kira da a bar ƙananan hukumomi su yi aiki yadda ya dace domin gazawarsu na daga cikin ababen da ke haifar wa tsaro cikas a sassan ƙasar.

By Babaji