Majalisar Ɗinkin Duniya na neman a daidaita taswirar Afirka ta gaskiya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Juma’a Majalisar Ɗinkin Duniya ta gudanar da zaɓe don nuna goyon baya ga wani yunƙuri na ƙasashen Afirka da dama da ke neman a daidaita taswirar nahiyar ta gaskiya da kuma rage arewacin Amurka da Turai.

Hakan na da nufin gabatarwa ta daidai akan faɗin ƙasa, inda aka samu ƙasashe 164 sun nuna goyon baya yayin da Amurka da wasu shida suka ƙi bayar da goyon baya.

Wannan matsaya ta nuna cewa sabuwar taswirar wadda aka sani da “The Equal Earth cartographic projection”, zaɓi ne kan inganta haƙiƙanin gabatarwar taswirar duniya.

Ta kuma roƙi ƙasashen majalisar da su bi sabuwar taswirar a madadin wadda aka saba amfani da ita, wadda masanin zanen taswira na Flemish, Gerardus Mercator ya samar a 1569.

Ministan harkokin wajen Togo, Robert Dussey, wanda ya jagoranci wannan mataki, ya ce taswirai na taimaka wa ilimi da faɗaɗa matakin nazari da tasiri ga fahimtar ɓangarorin haɗaka.

Saidai Amurka a nata ɓangaren, ta caccaki wannan yunƙuri inda ta ce hakan na ɗaya daga cikin ababen da ke haifarwa majalisar koma-baya. A cewarta, a madadin mayar da hankali kan muhimman matsaloli, MƊD ta koma tattaunawa kan taswirar da aka tsara tun a ƙarni na 16, kamar yadda wakilin Amurka, Yaryna Ferencevych ya bayyana.

By Babaji