Raunin Osimhen ya haifar wa Super Eagles tsaiko yayin da Iheanacho da Usor ke ƙoƙarin koma wa tawagar

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kocin Nijeriya, Eric Chelle ya shiga mawuyacin hali a ranar Juma’a bayan da Victor Osimhen ya samu wani rauni da ya tilasta masa fita daga fili yayin da ake tsaka da wasa, a daidai lokacin da Kelechi Iheanacho da Moses Usor suke cigaba da matsawa domin ganin Super Eagles ta kira su.

An fitar da Osimhen ne daga filin wasa a minti na 33 yayin da Galatasaray ta doke Istanbul Basaksehir da ci 3 da 2 a karawarsu ta gasar Super Lig, jim-kaɗan bayan zura ƙwallonsa na shida a wannan kakar.

Ana ganin hakan a matsayin abin da zai haifar wa tawagar Super Eagles tsaiko yayin wasanninta na neman gurbi a Kofin Ƙasashen Afirka na 2027 da ke tafe.

A yanzu dai koci Chelle zai fuskanci matsi kan raunin zakaran ɗan wasan, inda Super Eagles za ta karɓi baƙuncin Madagascar a ranar 25 ga Satumba kafin ta yi tattaki zuwa Guinea-Bissau a ranar 29 ga Satumba a jerin wasannin neman gurbi a kofin Afirka na 2027.

By Babaji