Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa, ya tabbatar wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu cewa al’ummar Jihar Katsina na tare da shi, yana mai bayyana cewa zai samu nasara cikin sauƙi a zaɓen 2027.
Gwamna Raɗɗa ya bayyana hakan ne a yayin taron ƙaddamar da motoci 34 na yaƙin neman zaɓe na PBAT Door-to-Door Movement Tinubu/Shettima 2027, tare da ƙaddamar da shugabannin ƙungiyar a Jihar Katsina.
A cikin jawabin nasa, Gwamna Raɗɗa ya ce Tinubu, kada ka ji komai. Jihar Katsina taka ce kuma cikin sauƙi za ka ci zaɓenka da rinjaye,
Ya kuma bayyana cewa ’yan jam’iyyar APC a Jihar Katsina suna da haɗin kai, yana mai cewa dukkan ’yan jam’iyyar uwa ɗaya da uba ɗaya ne”(A akushi ɗaya muke cin abincin) Dikko yace.
A cewar gwamnan, duk ɗan takarar da APC ta tsayar a jihar zai samu cikakken goyon bayan mambobin jam’iyyar.
Gwamna Raɗɗa ya jaddada cewa haɗin kan ’yan APC a Jihar Katsina zai taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da nasarar jam’iyyar da ’yan takararta a zaɓukan da ke tafe.
Za a bayar da waɗannan motoci da High Chief TOMPOLO ya samar, domin gudanar da yaƙin neman zaɓen APC a Jihar Katsina, wanda zai haɗa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Malam Dikko Umar Raɗɗa, Sanatoci, ’Yan majalisun tarayya da na dokoki.
Waɗannan motoci suna ɗauke da janareta da kayan sauti, domin gudanar da yaƙin neman zaɓen da ke tafe na shekarar 2027.
Bikin da ya gudana a filing taro na People Square Katsina ya sami halartar Tampolo da manya jami’an gwamnati na ƙasa da na jiha.
