Daga AISHA ASAS
Wakar Davido mai suna B4 B4, wadda ya hada da Mayorkun da FOLA, ta sake riƙe matsayi na daya a jadawalin waƙoƙin Najeriya, inda ta shafe makonni huɗu a jere tana saman Official Nigeria Top 100.
Waƙar ta ci gaba da samun gagarumar karɓuwa a tsakanin masu sauraro, inda bayanan jadawalin suka nuna cewa ta samu sama da miliyan 3.29 na sauraron waƙar ta hanyar yanar gizo, tare da kusan miliyan 80 na isar rediyo a cikin makon.
Sai dai yayin da Davido ke ci gaba da riƙe matsayinsa, Ayra Starr da ZAYN sun ƙara matsowa kusa da shi da wakarsu Heaven Baby, wadda ta haura zuwa matsayi na biyu.
Hakan ya sanya tseren saman jadawalin ya ƙara ɗaukar hankali, domin yanzu bambancin dake tsakanin manyan waƙoƙin mawaƙan biyu ya ƙara zama abin da masoyan wakokin Najeriya ke sa ido a kai.
B4 B4 ta samu nasarar ci gaba da riƙe matsayi na ɗaya, yayin da Heaven Baby ke nuna karfin da take da shi tun bayan fitowarta, lamarin da ya sanya Davido da Ayra Starr cikin manyan sunayen da suka fi ɗaukar hankalin masu sauraron waƙoƙin Najeriya a wannan lokaci.
