‘Yan sanda sun kama ɓarayin waya a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Rundunar ’yan sandan Jihar Katsina ta kama mutane uku da ake zargi da hannu wajen kutsen gida, sata, karɓar kayan sata da haɗa baki wajen aikata laifi.

Lamarin ya faru ne a Ƙofar Marusa, Katsina, inda wasu ’yan bindiga suka kutsa cikin wani gida da tsakar dare, suka sace wayoyin hannu daban-daban, turare da kuma zoben zinariya.

Kamar yadda jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya sanar,binciken ’yan sanda ya kai ga kama Abubakar Abbas, wanda aka fi sani da “Buti”, mai shekaru 24, inda aka same shi da wayar iPhone XR da ake zargin cikin kayan da aka sace.

Daga bisani an kama wasu mutane biyu, Yusuf Alasan, mai shekaru 19, da Aminu Armaya’u, mai shekaru 21, waɗanda rundunar ta ce sun amsa hannu a laifin.

Aminu Armaya’u ya bayyana cewa a baya sun haɗa baki wajen satar babura biyu a Janbango, waɗanda aka sayar da su kan Naira 660,000.

Rundunar ta ce tana ci gaba da neman sauran waɗanda ake zargi da hannu a cikin laifukan, tare da ƙoƙarin kwato sauran kayayyakin da aka sace.

Kwamishinan ’Yan Sandan Katsina, CP Ali Umar Fage, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da binciken tare da umartar a kammala bincike domin gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu.

By ukarofi

Leave a Reply