APC a Osun ta janye ƙarar ƙalubalantar nasarar sake zaɓar Gwamna Adeleke

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jam’iyyar APC a Jihar Osun, ta fitar da sanarwar janye ƙarar da ta shigar a gaban Kotun Ƙorafin Zaɓe ta ƙorafin ƙalubalantar nasarar Gwamna Ademola Adeleke a zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar a wannan shekarar.

Hakan na zuwa ne kwana guda da kotun ta wallafa ƙorafe-ƙorafe guda biyu na ƙalubalantar sakamakon zaɓen da aka gudanar a ranar 15 ga Agusta, waɗanda jam’iyyun APC da PDP suka shigar mata. An sanya wa takardun biyun kwanan wata 5 ga Satumba, 2026.

Sanarwar janye ƙarar ta APC na ƙunshe ne a wata takarda da Lauya Seyi Oyagbile ya fitar bayan cece-kuce da kokawa kan ƙorafin. Da fari, ya ce sun shigar da ƙorafin ne ƙarƙashin umarnin mataimakin ɗan takarar gwamnan jam’iyyar, Benjamin Adereti, wanda ya ce ya sanya wa takardar hannu a gaban kotun.

Saidai, daga bisani APC ta yi watsi da ƙorafin da kotun ta wallafa a allon sanarwarta a ranar Litinin, inda ta yi iƙirarin cewa babu wanda ya amince da haka tsakanin ɗan takarar jam’iyyar da tawagar shari’arsa.

Wani babban lauya daga cikin tawagar mai suna Dakta Abiodun Layonu (SAN) a wata sanarwa, ya ce ba su suka gabatar da ƙorafin ba sannan bai samun sahalewar shugabancin jam’iyyar ba, yayin da shi ma kakakin yaƙin neman zaɓen APC na jihar, Remi Omowaye ya kirayi al’umma da su yi watsi da takardar da kotun ta gabatar.

Wannan mataki ya kawo ƙarshen batun shigar da ƙorafin ƙalubalantar nasarar Gwamna Adeleke bayan lauyoyin APC sun musanta amincewa da hakan a bainar jama’a.

By Babaji