Gwamnatin Tarayya da NYSC za su fito da tsarin adana bayanai domin daƙile takardun bogi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta ce tana shirin ƙara haɗa tsarin adana bayanan ilimi na zamani da na Hukumar Kula da Hidimar Matasa ta ƙasa (NYSC), domin yaƙi da safarar takardun shaidar karatu na bogi, ƙarfafa tantance cancantar masu digiri da kuma tabbatar da cewa ba a hana waɗanda suka yi karatu na gaskiya damar samun ayyuka ba.

News Point Nigeria ta ruwaito cewa Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin wata ganawa da Darakta-Janar na NYSC, Birgediya-Janar Olakunle Nafiu, wanda ya jagoranci tawagar hukumar zuwa ma’aikatar da ke Abuja.

An bayyana bayanan taron da jawabin ministan ne a cikin wata sanarwa da Mai Ba Ministan Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai da Sadarwa, Ikharo Attah, ya fitar.

Alausa ya ce sauye-sauyen zamani da ake aiwatarwa a fannin ilimi ƙarƙashin ajandar Renewed Hope ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu, na da nufin rufe gibin da ke cikin tsarin adanawa da tantance bayanan ilimi, tare da sauƙaƙa tantance sahihancin takardun shaidar karatu a dukkan matakan tsarin ilimi.

Ya ce, “Sauya tsarin ilimi na Nijeriya zuwa na zamani ƙarƙashin ajandar Renewed Hope ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ƙarfafa sahihancin takardun shaidar karatu, daƙile safarar takardun bogi tare da tabbatar da cewa ɗalibai da waɗanda suka kammala karatu na gaskiya ba su fuskanci rashin adalci ba.”

Ministan ya bayyana cewa Nigerian Education Repository Data Bank (NERD) na tattarawa da tantance takardun shaidar jami’o’i, tare da bibiyar ɗalibai a dukkan matakan tsarin ilimi da kuma tallafa wa manyan makarantun gaba da sakandare ta hanyar jami’an da aka ɗora wa alhakin taimaka musu.

Ya ƙara da cewa Nigerian Education Data Infrastructure (NEDI) zai haɗa bayanan ɗalibai daga matakai daban-daban na tafiyar karatunsu.

Alausa ya kuma bayyana cewa ma’aikatar ta mayar da ayyukan Education Support Services gaba ɗaya zuwa tsarin zamani, ciki har da tantance takardun shaidar karatu da kuma hanyoyin da suka shafi masu neman karatu daga ƙasashen waje.

Ya ce, “Ana ci gaba da tattaunawa da NYSC kan wani tsarin sadarwa na fasaha (API), wanda zai ba da damar tantance bayanai cikin sauri da kuma musayar bayanan da suka dace tsakanin cibiyoyin biyu ba tare da tangarda ba.”

Ministan ya ce sauye-sauyen za su taimaka wajen magance matsalolin gudanarwa da na bayanai waɗanda a baya suka hana wasu waɗanda suka cancanta shiga hidimar ƙasa da kuma samun cikakkiyar dama a kasuwar ayyuka.

Ya bayyana cewa bambance-bambancen sunaye, matsalolin da suka shafi waɗanda suka yi National Diploma (ND) na ɗan lokaci, da kuma shigar da masu National Certificate in Education (NCE) zuwa shirye-shiryen Higher National Diploma (HND) na daga cikin matsalolin da ke buƙatar gaggauta magance su.

Alausa ya ce ma’aikatar za ta yi aiki tare da National Board for Technical Education (NBTE), Joint Admissions and Matriculation Board (JAMB), National Identity Management Commission (NIMC) da sauran masu ruwa da tsaki domin samar da mafita mai ɗorewa.

Ya ce matakan da ake shirin ɗauka sun haɗa da samar da Lambar Shaidar ɗalibi ta ƙasa (National Learner Identification Number) da kuma kafa tsari guda ɗaya na rubuta da tsara sunaye a cikin bayanan ilimi da na shaidar zama ɗan ƙasa na hukumomin gwamnati.

Ministan ya ce irin wannan tsari zai tabbatar da kafa ingantaccen bayanin shaida tun daga farkon tafiyar karatun ɗalibi, tare da rage bambance-bambancen bayanai da ka iya haifar da matsala ga wanda ya kammala karatu daga baya.

Ya kuma ce gwamnati ta ƙara ƙarfafa matakan yaƙi da magudin jarabawa, ciki har da fallasa tambayoyin jarabawa kafin lokaci, yana mai jaddada cewa ya kamata a ci gaba da wannan nasara tare da faɗaɗa matakan zuwa manyan makarantun gaba da sakandare.

Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da Gwamnatin Tarayya ke ƙara tsaurara matakan tantance sahihancin takardun shaidar karatu da ake amfani da su wajen neman aiki da kuma gudanar da aikin yi wa ƙasa hidima.

A watan Satumban 2025, gwamnati ta umarci ma’aikatu, hukumomi da sassan gwamnati da su fara amfani da National Credential Verification Service wajen tantance takardun shaidar karatun ma’aikata da sabbin ma’aikata. An tsara fara aiwatar da manufar ne a watan Oktoban 2025.

Daga bisani, gwamnati ta ɗauki matakin sanya tantance takardun shaidar NERD cikin tsarin tantance waɗanda za su shiga shirin NYSC.

A watan Maris na 2026, Alausa ya ce ana sa ran waɗanda za su shiga NYSC za su gabatar da takardun NERD da ke tabbatar da sahihancin cancantar karatunsu kafin yin rajistar shiga aikin yi wa ƙasa hidima na dole.

Haka kuma, NYSC ta sanar a watan Yunin 2026 cewa za ta aiwatar da wannan buƙata tsaf, a wani mataki na hana waɗanda ba su cancanta ba ko kuma masu takardun bogi shiga tsarin yi wa ƙasa hidima.

Damuwar da ake da ita kan takardun shaidar karatu na bogi ta kuma bayyana a cikin bincike da gurfanar da wasu mutane a gaban kotu a baya-bayan nan.

A watan Nuwamban 2025, tsohon Magatakardar JAMB, Farfesa Is-haƙ Oloyede, ya bayyana cewa kimanin ’yan takara 15,000 ne ake zargin sun ƙirƙira takardun shaidar karɓar gurbin karatu domin su samu damar shiga tsarin NYSC.

Haka kuma, binciken Gwamnatin Tarayya kan takardun shaidar karatun tsohon Ministan ƙirƙire-ƙirƙire, Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji, ya kai ga wani kwamitin bincike da ya bayyana a watan Maris na 2026 cewa takardar shaidar digirinsa daga Jami’ar Nijeriya, Nsukka, ta kasance ta bogi.

Batun ya kuma shafi wasu tambayoyi game da takardar shaidar NYSC.

A nasa ɓangaren, Nafiu ya yaba wa ma’aikatar kan sauye-sauyen da take aiwatarwa na zamani, tare da yin alkawarin cewa NYSC za ta ci gaba da tallafa wa sauye-sauyen da ake yi a fannin ilimi.

Ya ce NYSC ta fara amfani da tsarin zamani tun daga shekarar 2014, inda ta samar da tsare-tsare da ke ba da ingantattun bayanai kan waɗanda ke aikin yi wa ƙasa hidima da kuma yadda ake tura su wuraren aiki.

Nafiu ya bayyana cewa hukumar ta bi umarnin Majalisar Zartarwa ta Tarayya na yin haɗin gwiwa da Nigerian Education Repository Data Bank, kuma a shirye take ta ƙara zurfafa haɗin gwiwar da ke tsakaninta da ma’aikatar.

Shugaban NYSC ya ce amfani da fasaha ya ƙara inganta sahihancin ayyukan hukumar, yana mai cewa ƙaddamar da lambobin ƙR codes ya “kusan kawo ƙarshen kwafin takardu” a cikin NYSC.

By ukarofi