El-Rufai ya nemi diyyar Naira biliyan 10 da neman afuwa daga ministan tsaro

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya nemi ministan tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya biya shi Naira biliyan 10 tare da neman afuwarsa a bainar jama’a kan kalaman da ya ce sun bata masa suna.

Lauyoyin El-Rufai ne su ka gabatar da bukatar a wata wasikar gargadi kafin daukar matakin shari’a da suka aika wa ministan ranar Litinin, 7 ga Satumba, 2026.

Bukatar ta biyo bayan bayyanar Musa a shirin Politics Today na Channels Television ranar 3 ga Satumba, inda ya yi magana kan matsalar tsaro a Kaduna tare da yin zarge-zarge kan tsohon gwamnan.

Lauyoyin sun ce kalaman ministan sun nuna El-Rufai a matsayin wanda ya shirya kisan mutane, ya biya ’yan bindiga, kuma ya yi amfani da rusa gidaje wajen gallaza wa abokan hamayyarsa.

Sun bukaci Musa ya janye kalaman, ya gyara su sannan ya nemi afuwar El-Rufai a cikin shirin da aka yi kalaman, tare da wallafa afuwar a jaridun kasa.

Lauyoyin sun kuma musanta zargin cewa El-Rufai ya taba biyan ’yan bindiga, suna cewa tsohon gwamnan ya sha nanata cewa ba zai taba tattaunawa ko biyan ’yan bindiga ba.

Sun ce kuma rushe-rushen gine-ginen da aka yi a lokacin mulkinsa an gudanar da su ne bisa doka kuma saboda buƙatun jama’a.

Lauyoyin sun bai wa Ministan Tsaron wa’adin kwanaki bakwai da ya cika bukatunsu, inda suka gargadi cewa za su garzaya kotu idan ya ki.

By ukarofi

Leave a Reply