NNPCL na shirin gabatar da gidajen mai masu aiki da na’ura kai-tsaye

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Babban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL) na shirin fara amfani da sabon tsarin zamani na sayen man fetur a wasu gidajen mansa ta yadda direbobi za su iya biyan kuɗin mai ta manhajar waya kuma su zuba man da kansu, wanda ake sa ran ya fara aiki nan da wata shida.

A sabon tsarin, mai mota zai sauke manhajar sayen mai, ya zaɓi irin man da yake so da gidan man da ke da tsarin zuba mai da kai, sannan ya biya kuɗin man ta manhajar. Bayan biyan kuɗin, za a ba shi lamba mai lambobi takwas, wadda zai saka a na’urar famfon mai domin fara zuba man.

Mataimakin Shugaban NNPC mai kula da harkokin rarraba man fetur, Mumuni Dagazau ne ya bayyana hakan ranar Alhamis a Abuja yayin ƙaddamar da wani gidan mai mai sarrafa kai da kansa tare da tashar cajin motocin lantarki.

Dagazau ya ce shirin na da nufin sauya gidajen mai na yau da kullum zuwa cibiyoyin samar da makamashi, waɗanda za su haɗa wutar lantarki, gas da man fetur tare da tashoshin cajin motocin lantarki. Ya ce NNPC na shirin ƙaddamar da irin waɗannan gidajen mai guda biyu a Kano, yayin da ake da wasu guda huɗu ko biyar a Abuja, sannan za a faɗaɗa shirin zuwa sauran sassan ƙasar.

Ya bayyana cewa, tsarin zai bai wa abokan hulɗa damar zuba man fetur da kansu, har da dare, ta hanyar biyan kuɗi na zamani, yayin da ma’aikata za su kasance domin taimakawa.

By Babaji

Leave a Reply