Sojoji sun fara bincike bayan zargin babban jami’i da cin zarafin kurma maras galihu a Taraba

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

An zargi wani babban jami’in soja mai suna Kyaftin Etim Essien da cin zarafin wata maras galihu a Jihar Taraba, inda rundunar soji ta ƙaddamar da bincike kan al’amarin.

Yarinyar mai shekaru 13, wadda kurma ce da ba ta magana, an zargi jami’in da yin lalata da ita a lokuta da dama a lokacin da take ƙarƙashin kulawar iyalansa.

Akan haka ne Ma’aikatar kula da Harkokin Mata da Ci-gaban Yara da Hukumar kula da ‘Yancin Ɗan-adam ta Ƙasa (NHRC) suka fara bincike, inda suka buƙaci Rundunar Sojin Nijeriya ta ɗauki ladabtarwa akan jami’in.

A wata sanarwa da Mataimakin Daraktan Riƙo na rundunar na Sashi na 3, Olumide Olukoya ya fitar a ranar Juma’a, an tabbatar da cewa rundunar ta fara bincike a kai wajen gano haƙiƙanin al’amarin zargin. Ya ce, rundunar tana ɗaukar al’amarin cin zarafin lalata musamman akan marasa galihu da matuƙar muhimmanci, tana mai cewa za ta tabbatar da ɗaukar matakin doka akan jami’in muddin aka same shi da hannu a laifin.

Olukoya ya ƙara da cewa, rundunar tana cigaba da ƙoƙarin biyayya ga hukunce-hukuncen doka da bayar da kariya ga ‘yanci da mutuncin kowane ɓangare wajen tabbatar da gaskiya da adalci.

Saboda haka ne kuma rundunar ta yi kira ga al’umma da su ƙaurace wa yaɗa jita-jita da yaɗa bayanan da ba su tabbata ba kan al’amarin har sai an fitar da sakamakon bincike, tana mai cewa za ta cigaba da bai wa hukumomin masu ruwa da tsaki a kai haɗin kai ta yadda za a tabbatar da adalci yayin binciken.

By ukarofi

Leave a Reply