‘Yan wasan ƙwallon ƙafa uku daga Katsina sun sanya hannu a wani kulob na ƙasar Belarus

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

‘Yan wasan ƙwallon ƙafar na Football Academy su uku daga Katsina sun sanya hannu na buga tamola a ƙungiyar Prolex da ke ƙasar Belarus.

Yan wasan sun haɗa da Isma’il Nuhu,Alhassan Muhammad Sherif da Aliyu Abdullahi.

Ana sa ran za su fara buga ƙwallon a matsayin abin ƙwararru bayan da suka kammala samun horo a ƙungiyar ta FC Torpedo na ƙasar.

Wannan cigaba da aka samu ya nuna mahimmancin kulla da ƙwallon matasa na Football Academy,ya kuma ƙara gano
waɗanda suna Iya samun damar buga wasa a Ƙasashen waje.

Kamar yadda sanarwa ta fito daga Football Academy,za su cigaba da sa ido ga yan wasan Academy domin gano haziƙai da nan gaba za su buga kwallon kafa ƙasashen duniya da kuma wakiltar ƙasar su a gasar wasa na Afrika da duniya baki ɗaya.

By ukarofi

Leave a Reply