Daga JOHN D. WADA a Lafia
Wani mummunan iftila’i ya afku a jihar Nasarawa inda wasu magoya bayan ɗan takarar gwamnan jihar Nasarawa na jam’iyyar SDP wato Adamu Muhammad Abubakar su shida suka rasa rayukansu sakamakon wani mummunan hatsarin mota a kan gadar sama ta Lafia babbar birnin jihar a jiya Talata.
Wakilin mu a jihar ta Nasarawa wanda ya ziyarci inda haɗarin ya auku ya ruwaito cewa waɗanda hatsarin ya rutsa da su, magoya bayan ɗan takarar gwamna na SDP ne kuma tsohon Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya Mohammed Abubakar Adamu. Suna kan hanyarsu ce ta zuwa garin Awe na ƙaramar hukumar Awe a jihar domin wani taron gangamin siyasa lokacin da lamarin ya faru.
Da yake tabbatar da haɗarin, daraktan yaɗa labarai da sadarwa da dabarun yaƙin neman zaɓen na ƙungiyar yaƙin neman zaɓen Abubakar Adamu wato High Chief Otaru Douglas yace a yanzu haka iyalan yaƙin neman zaɓen da jam’iyyar ta SDP a jihar baki ɗaya sun shiga cikin alhini.
Douglas ya bayyana cewa duk da bai samu izinin fitar da sanarwar lamarin a hukumance ba domin har yanzu ɗan takarar majalisar yaƙin neman zaɓen da magoya bayansa na cikin jimami shima.
Amma a cewarsa hatsarin wani hatsari ne na rashin sa’a da zai iya faruwa ga kowa.
“Abin da zan iya faɗa a yanzu kawai shi ne muna rokon Allah ya jiƙan mamata ya kuma baiwa waɗanda suka jikkata saurin warkewa. IGP da matarsa na tare da iyalan mamatan. Sa’annan mun yin addu’ar wannan fitar rai mai raɗaɗi ta zama farkon zaman lafiya da cigaba ga iyalansu,” in ji shi.
A kan adadin waɗanda suka mutu kuwa sai Otaru yace “Rahoton da muka samu kawo yanzu dai an ce mutum shida ne wato rahoton da aka bani kenan a hukumance mutum shida. Amma kuma akwai waɗanda suka jikkata da ke cigaba da samun kulawar likitoti a asibitoti daban daban da ke nan birnin Lafia yayin da aka kuma ajiye gawarwakin mamatan.”
Wakilin namu ya kuma bayyana cewa a halin yanzu dai mummunan hatsarin yana cigaba da jawo ta’aziyya daga ciki da wajen jihar inda da dama kuma ke kira ga ƙungiyoyin siyasa da su yi taka-tsantsan wajen jigilar magoya baya zuwa filayen yaƙin neman zaɓe da sauran bukukuwa a lokacin nan da aka fara siyasa gadam-gadam don hana aukuwar irin wannan bala’in nan gaba.
