Daga AISHA ASAS
Marubuci, mawaƙi kuma manomi ɗan Amurka Wendell Berry ya rasu yana da shekara 92, bayan shafe tsawon rayuwarsa yana rubuce-rubuce kan noma, muhalli da rayuwar karkara, musamman a Jihar Kentucky da ya fito.
Berry, wanda ya shahara da littattafai, waƙoƙi da makaloli, ya mayar da rayuwar manoma da al’ummomin karkara wani babban jigo a cikin ayyukansa. Rubuce-rubucensa sun kuma yi kakkausar suka ga yadda bunƙasar masana’antu ke sauya alaƙar mutane da ƙasa da muhalli.
A cikin ayyukansa akwai ‘The Unsettling of America’ da ‘The Gift of Good Land’, yayin da littattafan almara kamar ‘Jayber Crow’ suka mayar da rayuwar mutanen karkara da dangantakarsu da juna wani muhimmin ɓangare na labarin.
Berry bai tsaya a rubuce-rubuce kawai ba. A matsayinsa na manomi, ya yi rayuwa a ƙasar Kentucky kuma ya shafe shekaru yana magana kan muhimmancin noma mai ɗorewa da kare ƙasa daga illolin tsarin noma da masana’antu da ya yi imanin cewa yana iya lalata al’ummomin karkara.
Ra’ayoyinsa sun sa aka ɗauke shi a matsayin ɗaya daga cikin fitattun masu kare salon rayuwar karkara da noma mai ɗorewa a Amurka. Ya samu lambobin yabo da dama saboda rubuce-rubucensa da aikinsa na kare muhalli da al’ummomin manoma.
Berry ya rasu a gidansa da ke Port Royal, Kentucky, ranar Litinin, yana da shekara 92, yayin da ya bar ɗimbin masoya da ‘yan uwansa cike da alhinin rashinsa, wanda suka kira da babban rashi da ba a iya samun cike shi
