
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Yayin da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ke shirin zuwa gaisuwar ta’aziyyar ga iyalan marigayi Bamanga Tukur, Rundunar ‘Yan sanda a Jihar Adamawa ta tura jami’ai na musamman domin daƙile tarzoma da tankokin yaƙi zuwa wasu yankuna a Yola, Babban Birnin jihar.
Rahotanni sun bayyana cewa rundunar ta ɗauki wannan mataki ne bisa ziyarar da mataimakin shugaban ƙasar zai kai zuwa jihar a hukumance. A wata sanarwa da SP Suleiman Nguroje, wato kakakin rundunar ya fitar a ranar Alhamis, ya ce ‘yan sandan sun ɗauki matakan ne a sassan Yola da wasu wurare a jihar.
A cewar sanarwar, Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Kabir Hassan ne ya bayar da umarnin a tura jami’an, inda ta ƙara da cewa jami’an da aikin ya shafa sun haɗa da ‘yan sandan mobile, jami’an yaƙi da garkuwa, na leƙen asiri, na kula da zirga-zirgar ababen hawa da DPO daga ofisoshi daban-daban domin tabbatar da cikakken tsaro yayin ziyarar mataimakin shugaban ƙasar.
Kwamishinan ya kuma ce, za a samu sauyin yanayin zirga-zirga da atisayen shingen bincike acikin babban birnin jihar. Ya shawarci al’umma da su bai wa jami’an tsaro haɗin kai da kuma kasancewa masu biyayya ga doka da oda yayin ziyarar Shettima.
Haka kuma, kwamishinan ya gargaɗi masu shirin aikata miyagun laifuka da su nesanta kansu daga wuraren da mataimakin shugaban ƙasar zai yi ziyarce-ziyarcen nasa, yana mai cewa hukumar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen kamawa da hukunta dukkan wanda aka samu da ƙoƙarin tayar da zaune-tsaye.
Kazalika, rundunar ta yi kira ga al’umma da su kasance masu lura da halin da ake ciki a yankunansu tare da ruwaito wa hukumomi dukkan wani abin zargi da suka gani akan lokaci domin ɗaukar matakan da suka dace, yana mai tabbatar musu da ƙoƙarin rundunar na bai wa rayuka da dukiyoyinsu kariya.
