Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
ƙasar Amurka ta miƙa wasu kayan aikin soji ga Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya, a wani mataki na ƙara ƙarfafa ƙarfin Nijeriya wajen yaƙi da ta’addanci a yankin.
Rundunar Sojin Amurka da ke kula da ayyukanta a Afirka (AFRICOM) ce ta bayyana hakan a wani saƙon da ta wallafa a shafinta na ɗ ranar Alhamis.
AFRICOM ta ce wani jirgin saman sojin Amurka kirar C-17 ne ya kawo kayan aikin zuwa Nijeriya a ƙarshen mako, ƙarƙashin yarjejeniyar sayar da kayan aikin soji tsakanin ƙasashen biyu.
Rundunar ta ce manufar wannan jigilar kayan aikin ita ce ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin Amurka da Nijeriya, tare da tallafa wa ƙoƙarin da Nijeriya ke yi na yaƙi da ta’addanci.
A cikin saƙon da AFRICOM ta wallafa, ta ce: “Haɗin gwiwa a aikace: Jirgin saman sojin Amurka ƙirar C-17 ya kai kayan aiki ga Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya a ƙarshen makon nan.
“Kayan aikin na cikin yarjejeniyar sayar da kayan aikin soji tsakanin ƙasashen biyu, wadda ke ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar Amurka da Nijeriya, tare da taimakawa ƙoƙarin Nijeriya na yaƙi da ta’addanci a yankin.”
Isar kayan aikin na zuwa ne a daidai lokacin da rundunar sojin Nijeriya ke ci gaba da ƙoƙarin magance matsalolin ta’addanci da sauran barazanar tsaro da ke addabar sassa daban-daban na ƙasar.
Amurka ta ci gaba da tallafa wa ƙoƙarin Nijeriya na inganta tsaro ta hanyar haɗin gwiwar soji, horar da jami’an tsaro da kuma samar da kayan aikin tsaro.
