Kotun Duniya: An zargi Malami da yi wa Nijeriya zagon-ƙasa kan rikicin wutar Mambilla

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kotun Sasantawa ta Ƙungiyar Kasuwanci ta Duniya (ICC) ta yi wasu manyan bayanai kan yadda aka gudanar da yarjejeniyar da ta shafi aikin samar da wutar lantarki na Mambilla a Jihar Taraba.

A hukuncin da ta fitar, kotun ta soki yadda tsohon Antoni Janar na Ƙasa, Abubakar Malami ya gudanar da wasu matakai tare da Leno Adesanya, waro Shugaban Sunrise Power, kan yarjejeniyar da ta tanadi biyan kamfanin dala miliyan 200, tare da yiwuwar ƙarin dala miliyan 200.

Kotun ta ce, yarjejeniyar ba ta samu amincewar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ba kuma rahoton ya nuna cewa Buhari ya ƙi amincewa da yarjejeniyar a rubuce, yayin da kotun ta kuma gano cewa an cigaba da neman amincewarsa a lokuta mabambanta.

Rahoton kotun ya kuma bayyana cewa yarjejeniyar ta saɓa wa manufofin jama’a na Nijeriya kuma ba za a iya tilasta wa gwamnati aiwatar da ita ba.

A rahoton da jaridar TheCable ta wallafa, kotun ta gano cewa Malami ya yi abin da ya ci karo da manufofi da martabar Nijeriya ta yadda ya karkata ga Sunrise a madadin Gwamnatin Tarayya saboda saɓa ƙa’idojin warware Dala miliyan 200, wanda ya ninka abin da Nijeriya za ta iya biya tare da yiwuwar ƙarin kuɗin ruwa na kaso goma a kowace shekara.

Ta kuma zargi tsohon ministan da bai wa Shugaba Muhammadu Buhari bayanan da ba haka suke ba kan tasirin kuɗi game da aikin akan Nijeriya. A ƙarshe, kotun ta ƙi amincewa da ikirarin Sunrise Power, tare da umartar kamfanin da Adesanya su mayar wa Nijeriya kusan Dala miliyan 11.8 na kuɗaɗen shari’a.

By Babaji

Leave a Reply