Shugaban NDC a Zamfara ya yi hasashen nasarar jam’iyyar a zaɓen 2027

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Shugaban jam’iyyar National Democratic Congress (NDC) a jihar Zamfara, Alhaji Surajo Garba Maikatako, ya bayyana Sanata Kabir Garba Marafa a matsayin ɗan takara mai ƙarfin gaske, wanda ke da goyon bayan jama’a da kuma ingantaccen shirin ci gaban jihar.

Maikatako ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Juma’a biyo bayan ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen gwamna na jam’iyyar a Gusau.

Ya bayyana fitowar Sanata Kabiru Garba a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar ta NDC a matsayin wani babban ci gaba mai tarihi da kuma alama bayyananniya ta nasarar da jam’iyyar NDC za ta samu a jihar a zaɓen da ke tafe.

Shugaban na NDC ya nuna ƙwarin gwiwar cewa za a rantsar da Sanata Marafa a matsayin Gwamnan jihar Zamfara a ranar 29 ga watan Mayun 2027 da ikon Allah.

A cewarsa, an samu halartar ɗimbin magoya baya, masu fatan alheri, da mazauna jihar baki ɗaya a wajen taron ƙaddamarwar, wanda a cewar sa ba a taɓa ganin irinsa ba.

Yawan mutanen da suka halarci taron shaida ce bayyananniya ta yadda Sanata Marafa ke da goyon bayan da ba za a iya misalta shi ba,” in ji Maikatako.

“Wannan taron jama’a da ba a taɓa ganin irinsa ba shaida ce da ba za a iya musantawa ba game da zurfin goyon baya da kuma amincewar da al’ummar jihar Zamfara ke nunawa ga takarar Sanata Marafa,” ya ƙara da cewa.

Maikatako ya kuma yaba wa Sanata Marafa bisa abin da ya kira karimci na musamman da ya nuna ga shugabannin jam’iyya da kuma mambobin kwamitin yaƙin neman zaɓen.

A wani mataki na sulhu, shugaban na NDC ya yi kira ga tsoffin magoya bayan jam’iyyar da suka bar jam’iyyar da suka koma tare da dawowa cikin jam’iyyar ta NDC duba da irin ƙaruwar ta a jihar.

“Ga magoya bayanmu da suka bar mu, ina muku kira na musamman daga zuciya, don Allah ku dawo gida don samun nasarar jam’iyyar mu,” in ji shi.

A cewarsa, Sanata Marafa ba shi da tarihin cin amanar mabiyansa.

Maikatako ya kuma yi kira ga sauran jam’iyyun siyasa a jihar Zamfara da su haɗa ƙarfi da ƙarfe da jam’iyyar NDC gabanin zaɓen 2027 bisa la’akari da farin jinin ta ga alummar jihar don kawo sauyi nagartacce.

By ukarofi

Leave a Reply