Daga JOHN D WADA a Lafia
Shugaban ƙaramar hukumar Kokona ta jihar Nasarawa Dr. Agbawu Mek Agbawu ya tallafawa mutane 110 da aka zaɓa daga gundumomi 11 na ƙaramar hukumar da kuɗi, babura da sauran kayayyaki da kuɗinsu ya haura naira miliyan 20.
Shirin tallafin ya haɗa da rabon fakitin kayan tsabtace mata wanda aka samu daga wajen uwargidan shugaban ƙasa wato Sanata Oluremi Tinubu da sabbin babura da zannuwa da tsabar kuɗi da dai sauran su.
Da yake jawabi a wajen ƙaddamar da shirin a Garaku ƙaramar hukumar Kokona Dr. Agbawu yace an ƙirƙiro shirin ne domin rage raɗaɗin talauci da samar da arziki ga al’umma a yankunan karkara.
Yace: “Ina matuƙar farin cikin maraba da ku da kuma yin jawabi a wajen ƙaddamar da wannan shiri na ƙarfafa tattalin arziki, wanda zai shafi gundumomi 11 na ƙaramar hukumar nan ta Kokona.
Yana da muhimmanci a lura cewa wannan shiri yana da matukar muhimmanci domin zai taimaka matuƙa wajen rage talauci da samar da arziki ga al’ummarmu a yankunan karkara.
A yau ina alfahari da cewa wannan gwamnati, ƙarƙashin jagorancin mai girma gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule ta yi ƙoƙari sosai wajen tabbatar da cewa bunƙasa ɗan Adam ya zama ginshiƙin gwamnatinsa.
Haka kuma dukkanin nasarorinmu a shirye-shirye da manufofi mun same su ne saboda zaman lafiya da ake da shi a ƙaramar hukumar. Don haka ina kira gare ku da ku ci gaba da kasancewa cikin zaman lafiya.
A ƙarshe ina kira ga waɗanda suka amfana da su yi amfani da waɗannan kayayyaki cikin hikima domin cigaban su ga kuma waɗanda ba su amfana ba a wannan karon su yi haƙuri domin nasu lokacin zai zo a zagaye na gaba.”
Taron ya samu halartar sakataren jam’iyyar APC a jihar Nasarawa Mista Yarus Dagusa wanda ya yaba wa shugaban ƙaramar hukumar bisa wannan karimci yana mai cewa tallafin zai rage raɗaɗin da talakawa ke ciki.
Dagusa ya kuma yi kira ga wadanda suka amfana da magoya bayan APC a yankin baki ɗaya da su saka masa da wannan alheri ta hanyar fitowa ƙwansu da kwarkwata su zaɓi dukkan ‘yan takarar jam’iyyar APC a zaɓe mai zuwa.
Haka kuma shugaban ƙaramar hukumar Wamba Hon. Ezekiel Musa Jagga ya yaba wa Hon. Mek Agbawu tare da kira ga waɗanda suka amfana da su yi amfani da kayayyakin ta hanyar da ya dace.
A nasa ɓangaren, kwamishinan Ilimi na jihar Dr. John Mamman ya ƙalubalanci sauran ‘yan siyasa da shugabanni da su yi koyi da irin wannan aikin alheri na Dr. Mek domin inganta rayuwar marasa ƙarfi a cikin al’umma.
Wasu daga cikin waɗanda suka amfana da suka yi magana a wajen taron sun nuna godiyarsu ga shugaban ƙaramar hukumar bisa tunawa da su a wannan lokaci na tsadar rayuwa suna mai alwashin yin amfani da kayayyakin ta hanyar da ya dace da kuma cigaba da marawa ƙaramar hukumar da gwamnatin jihar da kuma jam’iyya mai mulki ta APC baya.
Babban abin da ya ƙayatar a wajen taron shi ne gabatar da tallafin a alama ta hannun manyan baƙi da kuma nuna yadda ake amfani da kayan tsabtar na mata da ma’aikatan lafiya suka yi da sauran su.
