NGE ta gargaɗi hukumomin tsaro kan cin zarafin ’yan jarida

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kungiyar Editocin Jaridun Nijeriya (NGE) ta nuna damuwa kan yadda ake ƙara samun rahotannin cin zarafi, tsoratarwa da gurfanar da ’yan jarida da hukumomin tsaro ke yi, tana mai gargaɗin cewa irin waɗannan matakai na iya kawo cikas ga ’yancin aikin jarida da gudanar da aikin jarida bisa ƙa’ida.

Haka kuma, ƙungiyar ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) da su tabbatar da an samar da kyakkyawan yanayin da zai bai wa dukkan jam’iyyun siyasa da ’yan takararsu dama iri ɗaya gabanin babban zaɓen 2027.

A cikin wata sanarwa da Shugaban NGE, Eze Anaba, da Babban Sakataren ƙungiyar, Onuoha Ukeh, suka sanya wa hannu bayan kammala taron Kwamitin Zartarwa na dindindin da aka gudanar a Kano, editocin sun ce suna matuƙar damuwa da yadda ake amfani da dokokin yaƙi da laifukan intanet da wasu dokoki wajen taƙaita halastaccen aikin jarida.

NGE ta jaddada cewa ’yancin aikin jarida ginshiƙi ne mai muhimmanci na dimokuraɗiyya da kyakkyawan shugabanci, don haka bai kamata a yi amfani da dokoki wajen tauye haƙƙin ’yan jarida na gudanar da ayyukansu bisa ƙa’ida ba.

ƙungiyar ta buƙaci gwamnatoci a dukkan matakai da jama’a su mutunta ’yancin aikin jarida, tare da hulɗa da kafafen yaɗa labarai cikin fahimtar juna, maimakon yin barazana, tsoratarwa ko amfani da ƙarfi kan ’yan jarida da hukumomin kafafen yaɗa labarai.

NGE ta ce, duk wani mutum ko ƙungiya da ke da ƙorafi kan rahoton kafar yaɗa labarai ya kamata ya bi hanyoyin da aka tanada, musamman ta hannun Mai Sasanta Rikicin Kafafen Yaɗa Labarai (Media Ombudsman) da ƙungiyoyin masu buga jaridu, editoci, ’yan jarida da masu wallafa labarai ta intanet suka kafa tare.

Kungiyoyin da suka kafa wannan tsarin sun haɗa da ƙungiyar Masu Mallakar Jaridun Nijeriya (NPAN), ƙungiyar Editocin Jaridun Nijeriya (NGE), ƙungiyar ’Yan Jaridun Nijeriya (NUJ) da ƙungiyar Masu Wallafa Labaran Intanet na Kamfanoni (GOCOP).

Dangane da zaɓen 2027, editocin sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi da su samar da yanayin da zai bai wa dukkan jam’iyyun siyasa da ’yan takararsu damar gudanar da yakin neman zaɓe cikin ’yanci da adalci.

Sun kuma buƙaci hukumomi su bar jam’iyyun siyasa su nuna alamominsu a wuraren da doka ta amince da hakan, tare da yaɗa taken kamfen ɗinsu, ba tare da tsangwama ba.

Kungiyar ta kuma yi kira ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) da sauran hukumomin da ke da hannu wajen shirye-shiryen zaɓen 2027 da su tabbatar da ana mu’amala da dukkan jam’iyyu cikin adalci, ciki har da jam’iyyar da ke mulki da jam’iyyun adawa, ba tare da nuna bambanci ba.

A cewar editocin, samar da yanayin takara mai adalci ga kowa na da muhimmanci wajen ƙarfafa amincewar jama’a, da kuma tabbatar da sahihanci da mutuncin tsarin zaɓe.

Sun kuma buƙaci ’yan siyasa da jam’iyyunsu su mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi jama’a yayin yakin neman zaɓe, su guji kalaman da ka iya tayar da hankali, sannan su bi ƙa’idojin da aka gindaya wajen gudanar da kamfen.

NGE ta kuma buƙaci kafafen yaɗa labarai su ci gaba da kiyaye ƙa’idojin aikin jarida da ɗabi’arsa, tare da tabbatar da adalci, rashin son rai, sahihancin bayanai da bin gaskiya wajen gudanar da rahotanninsu.

A fannin tattalin arziki kuwa, ƙungiyar ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen tattalin arzikin da take yi, amma ta tabbatar da cewa jin daɗin ’yan Nijeriya shi ne ginshiƙin manufofi da matakan da take ɗauka.

Editocin sun kuma nuna damuwa kan yadda manyan hanyoyin gwamnatin tarayya ke ci gaba da lalacewa a sassa daban-daban na ƙasar, lamarin da suka ce ya jefa masu ababen hawa, matafiya da ’yan kasuwa cikin tsananin wahala.

Saboda haka, sun buƙaci Gwamnatin Tarayya ta ƙara ƙaimi wajen gyara, sake ginawa da kuma gina hanyoyi domin sauƙaƙa zirga-zirgar mutane da jigilar kayayyaki, tare da bunƙasa harkokin tattalin arziki.

ƙungiyar ta yaba wa hukumomin tsaro bisa nasarorin da suka samu wajen yaƙi da ta’addanci, ’yan bindiga da sauran nau’o’in laifuka.

Sai dai ta jaddada buƙatar hukumomin tsaron su ci gaba da gudanar da ayyukan haɗin gwiwa da ɗorewa domin tabbatar da samun zaman lafiya, tsaro da haɗin kan ƙasa na dindindin.

Kwamitin Zartarwa na dindindin na NGE ya kuma nuna godiya ga Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da gwamnatin jihar da al’ummar Kano bisa samar da kyakkyawan yanayi da ya ba da damar gudanar da taron ƙungiyar a jihar.

A ƙarshe, ƙungiyar ta sake jaddada cewa kyakkyawan shugabanci, jin daɗin jama’a, zaman lafiya, ci gaba da kuma mutunta ƙa’idojin dimokuraɗiyya su ne ginshiƙan samar da al’umma mai ɗorewa da wadata.

By ukarofi

Leave a Reply