Yadda sayar da hannun jarin matatar Dangote ya jawo cunkoso a manhajojin zuba jari

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Masu zuba jari a Nijeriya sun fuskanci matsalar shiga wasu manhajojin hada-hadar hannun jari, ciki har da Bamboo da Cowrywise, a ranar Litinin, yayin da dubban mutane suka yi tururuwa domin sayen hannun jarin Matatar Man Dangote.

Matsalar ta biyo bayan buɗe tallan hannun jarin ga jama’a ne a Kasuwar Hannun Jari ta Nijeriya (NGɗ) da misalin ƙarfe 9:30 na safe, inda ɗimbin masu zuba jari suka yi ƙoƙarin shiga manhajojin yanar gizo domin neman damar mallakar hannun jari a matatar.

Kamfanin Bamboo ya tabbatar da samun matsalar, yana mai cewa adadin mutanen da ke ƙoƙarin shiga manhajar ya zarce abin da aka saba samu.

Kamfanin ya bayyana a wata sanarwa da ya wallafa a dandalin ɗ cewa yawan masu amfani da ke ƙoƙarin shiga domin sayen hannun jarin Dangote ya yi matuƙar yawa, lamarin da ya sa wasu daga cikin masu amfani suka kasa shiga manhajar.

Bamboo ya ce ƙungiyar ƙwararrunsa na aiki domin magance matsalar tare da dawo da manhajar cikin yanayin aiki yadda ya kamata. Haka kuma, Cowrywise ta ce ta samu cunkoson masu amfani da manhajarta fiye da yadda aka saba, sakamakon yawan masu neman shiga domin sayen hannun jarin Dangote.

Kamfanin ya bayyana cewa ƙungiyar da ke kula da manhajar ta fara aiki kan matsalar domin dawo da komai yadda yake, tare da neman afuwar masu amfani da sabis ɗin kan cikas ɗin da suka fuskanta.

Cunkoson da aka samu a manhajojin hada-hadar hannun jari ya nuna irin yadda tallan hannun jarin Matatar Dangote ya jawo hankalin masu zuba jari a faɗin Nijeriya.

An buɗe damar da jama’a za su iya sayen hannun jarin matatar, inda wanda ya cancanta zai iya fara sayen hannun jari 10 kacal. Hakan ya ba talakawa da sauran masu zuba jari damar mallakar wani kaso na kamfanin ta hanyar manhajojin zuba jari da sauran hanyoyin da aka tanada.

Sha’awar masu zuba jari ta kuma bayyana a Kasuwar Hannun Jari ta Nieriya, inda rahotanni suka ce adadin hannun jarin da aka yi cinikinsa ya haura biliyan 1.4, yayin da darajar kasuwar ta ƙaru da kusan naira biliyan 100, kamar yadda wani saƙo da Kasuwar Hannun Jari ta Nijeriya ta wallafa, daga baya aka goge, ya nuna.

Wasu masu zuba jarin kuma sun nuna ɓacin ransu kan yadda wasu manhajojin suka yi jinkirin nuna damar sayen hannun jarin. Wata mai amfani da dandalin ɗ mai suna @Flashy_Vickie ta koka kan Afrinvest, tana cewa wasu manhajojin sun riga sun nuna hannun jarin Dangote, amma nasu har yanzu bai bayyana ba, lamarin da ta ce zai iya sa ta cire kuɗinta ta koma wata manhaja.

Me ya sa hannun jarin Dangote ya jawo hankalin masu zuba jari?

Tallan hannun jarin Matatar Dangote na daga cikin manyan harkokin kasuwar kuɗi da ake sa ido a kansu a Nijeriya, domin ya bai wa jama’a damar mallakar kaso a cikin babbar matatar mai a Afirka.

An gina matatar da ke Legas ne kan kuɗin da ya kai kusan dala biliyan 20. A halin yanzu tana da ikon tace gangar ɗanyen mai har 700,000 a kowace rana, yayin da ake shirin ƙara ƙarfin tacewar zuwa gangar miliyan 1.4 a kowace rana nan da shekarar 2029.

ƙididdigar kamfanin dillancin labarai na Reuters ta nuna cewa tallan hannun jarin ya sanya darajar matatar ta kai kusan dala biliyan 47. Wani ɗan jarida mai suna Ibrahim Abubakar ya ce yana shirin sayen kusan hannun jari 2,850, saboda a ganinsa matatar ta yi girma matuƙar da zai yi wuya ta gaza samun nasara.

Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, shi ma ya nuna cewa yana sa ran samun gagarumar buƙata daga masu zuba jari, musamman bayan wani tallan hannun jari na musamman da aka gudanar a watan Yuli, wanda rahotanni suka ce buƙatar masu neman sayen hannun jarin ta zarce yawan hannun jarin da ake da shi sau 3.7.

Matatar Dangote ta fara aiki a shekarar 2024, kuma tun daga lokacin ta zama ɗaya daga cikin manyan masu taka rawa a kasuwar man fetur ta Nijeriya, inda take samar da man fetur da aka tace a cikin gida tare da ƙara faɗaɗa fitar da kayayyakin man fetur zuwa ƙasashen waje, ciki har da man jiragen sama.

By ukarofi

Leave a Reply