2027: Duk da a APC nake ba zan hana mutane na su zaɓi ra’ayin su ba  — Na’Allah

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa, Sanata Bala Na’Allah, ya ce har yanzu ya na cikin jam’iyyar APC, amma zai goyi bayan duk jam’iyyar siyasar da al’ummarsa suka zaba a zaben 2027.

Na’Allah ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Arise Tɓ ranar Litinin.

Tsohon Sanatan ya ce a matsayinsa na ɗan jam’iyyar siyasa kuma mai bin tsarin dimokuradiyya, ba zai tilasta wa al’ummarsa goyon bayan wata jam’iyya da ba sa so ba.

Ya ce, “Ina cikin APC. Amma idan saboda wani dalili al’ummata suka yi imanin cewa APC ba ita ce jam’iyyar da suke son mara wa baya ba, ba zan yi amfani da matsayina na siyasa wajen tilasta musu abin da ba sa so ba.”

Na’Allah ya kara da cewa zai ci gaba da lura da sauye-sauyen siyasa da za su faru kafin zaben 2027, domin tantance wadanda ke da damar samun nasara.

A baya dai, Na’Allah ya janye daga takarar neman tikitin APC na Majalisar Dattawa, bayan da ya yi zargin cewa an riga an kammala sakamakon zaben fidda gwani tun kafin gudanar da shi.

By ukarofi

Leave a Reply