El-Rufa’i: Kotu ta za ta yi hukuncin shari’ar zargin naɗar hirar Ribaɗu a 26 ga Oktoba

Spread the love

Babbar Kotun Tarayya a Abuja, ta ayyana ranar 26 ga Oktoba, 2026 domin yanke hukunci kan buƙatar tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, ta cewa babu wata hujjar da za ta sa a ci gaba da shari’ar da ake yi masa.

El-Rufa’i yana fuskantar shari’a ne kan zargin kutse da naɗar kiran wayar Mai Ba wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkar Tsaro (NSA), da Hukumar Tsaro ta Farin kaya DSS ta shigar da shi a kansu. A zaman kotun da aka yi ranar Talata, lauyoyin gwamnati da na El-Rufai sun gabatar da hujjoji kan buƙatar a sallami tsohon gwamnan daga shari’ar ba tare da an tilasta masa ya gabatar da kariya ba.

Lauyan tsohon gwamnan, Mista Ekere ya buƙaci kotun ta amince da takardun buƙatar “no-case submission” da aka gabatar, sannan ya roƙi kotun ta sallami tsohon gwamnan daga tuhumar da ake masa.

Saidai, lauyan gwamnatin tarayya, Mista Oluwole Aladedoye, SAN, ya roƙi kotun da ta yi watsi da buƙatar El-Rufai, tare da umartar sa ya fara gabatar da kariyarsa. Aladedoye ya yi zargin cewa masu kare El-Rufa’i sun kauce wa wani muhimmin shaida (Exhibit B), wanda ya bayyana a matsayin wata sanarwa da ke ɗauke da iƙirarin tsohon gwamnan.

Bayan sauraron ɓangarorin biyu, Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta dage shari’ar zuwa 26 ga watan Oktoba domin yanke hukunci kan buƙatar El-Rufai. Tsohon gwamnan na fuskantar tuhume-tuhume guda biyar da gwamnatin tarayya ta shigar a kansa, waɗanda suka shafi zargin kutse da shiga cikin sadarwar NSA ba tare da izini ba.

Gwamnatin tarayya ta kuma zarge shi da samun damar wasu bayanan sirri ba tare da izini ba, da kuma taimakawa ko alaƙa da wasu mutanen da ake zargin sun kutsa cikin sadarwar Ribadu. Amma, tsohon gwamnan ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake yi masa akan shari’ar.

By Babaji

Leave a Reply