Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano
Hon. Ali Aminu Abubakar, wanda aka fi sani da Alin Dawaki, ɗan takarar kujerar Majalisar Dokokin Jihar Kano mai wakiltar ƙaramar Hukumar Dawakin Kudu a jam’iyyar ADC, ya bayyana ra’ayinsa cewa tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, shi ne ɗan takarar da ya kamata al’umma ta mara wa baya a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa.
Alin Dawaki ya bayyana hakan ne yayin wata hira da manema labarai a gidansa da ke Dawaki ranar Lahadi, inda ya ce Atiku Abubakar na da wani shiri da ya yi imanin zai sauƙaƙa wa ’yan Nijeriya halin matsin tattalin arzikin da suke ciki, ciki har da batun dawo da tallafin man fetur.
A cewarsa, Atiku Abubakar shi ne “jirgin fiton” al’ummar ƙasar da zai fitar da su daga halin da suke ciki, yana mai cewa tun bayan da jam’iyyar APC ta karɓi ragamar mulkin ƙasa, al’umma na fuskantar matsin tattalin arziki da ƙarin tsadar rayuwa.
Ya ce tun daga lokacin gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari zuwa gwamnatin yanzu, talakawa na ci gaba da fuskantar matsalolin tattalin arziki, yana mai bayyana buƙatar samun sauye-sauye a yadda ake tafiyar da mulkin ƙasar.
Dan takarar ya ce shirin Atiku na batun dawo da tallafin man fetur ya isa ya sa ’yan Nijeriya su yi la’akari da shi a lokacin zaɓe. Ya kuma bayyana rashin jin daɗinsa kan yadda farashin man fetur ke ci gaba da ƙaruwa, yana mai cewa bai kamata a riƙa yanke irin waɗannan matakai ba tare da la’akari da halin da ’yan ƙasa ke ciki ba.
Ya ƙara da cewa tun bayan cire tallafin man fetur, ’yan ƙasa ba su ga fa’idar da ake sa ran za su samu daga matakin ba, yana mai cewa gwamnati na ci gaba da neman rance domin gudanar da ayyukanta.
Bugu da ƙari, Alin Dawaki ya ce jam’iyyar ADC ta shirya tsaf domin fafatawa da jam’iyyar APC a zaɓe mai zuwa daga matakin tarayya zuwa ƙananan hukumomi, yana mai cewa manufarsu ita ce ganin an samu sauyin shugabanci da zai inganta rayuwar al’umma.
Ya yi kira ga ’yan ƙasa da su yi amfani da ‘yancinsu na zaɓe wajen tantance manufofin ’yan takara da jam’iyyu kafin su yanke shawarar wanda za su mara wa baya.
