Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano
Sarkin Tuken Kasuwar ’Yan Awaki da ke Unguwar Uku, a ƙaramar Hukumar Tarauni ta Jihar Kano, Alhaji Aliyu Suleiman, wanda aka fi sani da Baba Ali, ya yaba wa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa samar da hanya a kasuwar tare da sanya fitilun zamani masu amfani da hasken rana.
Sarkin ya ce samar da hanyar zai taimaka matuka wajen bunƙasa harkokin kasuwanci da kuma inganta yanayin gudanar da harkoki a kasuwar.
Alhaji Aliyu ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da wakilin Manhaja a kasuwar, inda ya ce gwamnatin jihar ta samar da wasu abubuwan ci gaba a kasuwar, musamman hanyar da aka samar da kuma sanya fitilun zamani domin ƙara inganta tsaro.
Ya ce tun bayan da aka naɗa shi a matsayin Sarkin Tuke a kasuwar, shi da sauran masu ruwa da tsaki sun taka muhimmiyar rawa wajen rage matsalolin ɓarna da satar kayayyaki a kasuwar.
A cewarsa, a baya ’yan kasuwa kan bar kayayyaki a kasuwar, amma idan suka dawo da safe sai su tarar an yi musu barna ko an sace wasu daga cikin kayayyakin. Ya ce sun yi ƙoƙarin magance wannan matsala tare da sauran masu ruwa da tsaki.
Alhaji Aliyu ya kuma bayyana damuwa kan yadda hauhawar farashin man fetur ke shafar harkokin kasuwancin dabbobi, inda ya ce kayayyakin ba sa tafiya kamar yadda suka saba a baya saboda ƙarin kuɗin sufuri da ake kashewa wajen kai dabbobi da sauran kayayyaki zuwa kasuwa.
Ya yi kira ga gwamnati da ta ƙara samar da fitilun zamani a kasuwar domin ƙara inganta tsaro, tare da neman a samar musu da ruwan sha, musamman ruwan da ake amfani da shi wajen shayar da dabbobin da ake sayarwa a kasuwar.
Haka kuma, ya yi kira ga sauran shugabanni da su riƙa mai da hankali wajen kula da buƙatun al’ummar da suke jagoranta, tare da ɗaukar matakan da za su inganta rayuwarsu da harkokin kasuwancinsu.
