Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce ’yan Nijeriya sun fara ganin saukar farashin sufuri sakamakon matakan da gwamnati ke ɗauka na amfani da makamashi mai rahusa wajen rage kuɗin zirga-zirga.
Shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne yayin da yake bayar da rahoto kan alƙawarin da ya yi na ganin an rage farashin sufuri daga ranar 1 ga Oktoban 2026.
A ranar 27 ga Agusta, Tinubu ya gana da gwamnonin jihohi 36, inda suka tattauna matakan da za su taimaka wajen rage farashin sufuri a faɗin ƙasar domin rage wa ’yan Nijeriya raɗaɗin matsin tattalin arziki.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, Tinubu ya ce bayan taron, an kafa kwamitin aiwatar da Shirin Samar da Sufuri Mai Sauƙin Kuɗi ta CNG na ƙasa, ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF). Ya ce, tuni kwamitin, PI-CNG da EV, jihohi da sauran masu ruwa da tsaki suka fara aiki wajen gano muhimman hanyoyin sufuri, tantance matakan da suka dace da kuma shirya abubuwan da ake buƙata domin rage kuɗin sufuri.
Tinubu ya kawo misalan wasu jihohi inda motocin sufuri masu amfani da CNG da motocin lantarki suka rage kuɗin sufuri, yana mai cewa ’yan Nijeriya sun fara jin tasirin hakan.
Ya ce, “A ranar 27 ga Agusta, na gana da gwamnonin jihohinmu 36, inda muka cimma matsaya kan wata manufa bayyananniya. Daga ranar 1 ga Oktoba, ya kamata ƙarin ’yan Nijeriya su fara ganin saukar farashin sufuri a zahiri.”
Ya ce buƙatar aiwatar da shirin ta ƙara zama cikin gaggawa sakamakon matsalar makamashi da duniya ke fuskanta a yanzu, yana mai cewa akwai shaidu daga sassan Nijeriya da ke nuna cewa makamashi mai rahusa na iya haifar da saukar farashin sufuri.
A Jihar Borno, ya ce motocin sufuri masu amfani da CNG da lantarki na jigilar fasinjoji kan kuɗi tsakanin N50 zuwa N100 a wasu hanyoyi, yayin da masu motocin kasuwanci ke karɓar tsakanin N300 da N600. A Kaduna kuma, motocin bas 100 masu amfani da CNG na yin zirga-zirga kyauta a manyan hanyoyi. Tinubu ya ce a shekararsu ta farko, motocin sun ɗauki fasinjoji kusan miliyan 3.2, lamarin da ya ceci matafiya sama da Naira biliyan 3.5 na kuɗin sufuri. A Oyo, motocin bas masu amfani da CNG da aka tura wa Pacesetter Transport sun rage kuɗin tafiyar Legas zuwa Ibadan daga kusan N8,000 zuwa N3,200 a farkon fara aikin.
A Adamawa, ya ce ayyukan sufuri masu amfani da madadin makamashi sun rage kuɗin mota da kusan kashi 50 cikin 100, daga N8,000 zuwa N4,000. A Enugu, inda aka tura motocin bas 100 masu amfani da CNG, an rage kuɗin tafiyar Enugu zuwa Nsukka daga N2,500 zuwa N1,500. A Plateau kuwa, motocin bas da gwamnati ke tallafawa na ɗaukar kusan fasinjoji 13,000 a kullum kan N200, yayin da masu motocin kasuwanci ke karɓar sama da N500.
Shugaban ƙasar ya ƙara da cewa, ta hanyar haɗin gwiwa da ƙungiyar Ma’aikatan Sufurin Haya ta ƙasa (NURTW), fasinjojin motocin kasuwanci da aka sauya su zuwa amfani da CNG a wasu hanyoyin Abuja na samun ragin kuɗin sufuri da kashi 40 cikin 100. Ya ce, kuɗin tafiyar Area 1 zuwa Gwagwalada ya ragu daga N1,500 zuwa N900; Nyanya daga N700 zuwa N420, yayin da Wuse ya ragu daga N400 zuwa N240.
Tinubu ya ce a Neja, fasinjojin da ke amfani da hanyar Suleja zuwa Abuja na biyan N550 maimakon kusan N800, yayin da Abia ta samar da motocin bas 40 masu amfani da lantarki, inda gwamnati ke tallafa musu da kashi 50 cikin 100 na kuɗin sufuri. “Waɗannan ba hasashe ba ne. ’Yan Nijeriya sun riga sun fara cin moriyar wannan ragi,” inji shi.
Tinubu ya yaba wa gwamnonin da suka rungumi amfani da CNG, amma ya ce har yanzu akwai ƙarin abin da ya kamata a yi, yana mai alƙawarin cewa Gwamnatin Tarayya za ta taimaka musu wajen faɗaɗa ayyukan.
Ya ce, rikice-rikicen da ke kawo cikas ga samar da makamashi a duniya na sake matsa farashin fetur da dizal, lamarin da ke ƙara kuɗin sufuri a ƙasashe daban-daban. “Nijeriya ba za ta iya sarrafa abubuwan da ke faruwa a kasuwannin makamashi na duniya ba. Amma kasancewar mu ƙasa mai arzikin gas na ba mu damar rage dogaro da waɗannan sauye-sauyen. Wannan shi ne abin da muke yi,” inji shi.
Ya ce cikin shekaru uku da suka gabata, gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen gina tsarin sufuri da ke amfani da CNG a faɗin Nijeriya. A cewarsa, sama da motoci 120,000 aka riga aka sauya su zuwa amfani da CNG, yayin da akwai cibiyoyin sauya motoci sama da 400 da aka amince da su, da kuma tashoshin cike CNG sama da 90 a faɗin ƙasar, waɗanda ke ci gaba da ƙaruwa.
Tinubu ya ce a irin wannan lokaci, bai kamata Nijeriya ta koma tsarin tallafin man fetur da ya ce ya cinye tiriliyoyin naira tare da barin tattalin arzikin ƙasar cikin dogaro da sauye-sauyen farashin ɗanyen mai na duniya ba.
Ya ce ya kamata a ƙara hanzarta amfani da hanyoyin makamashi masu rahusa da ake samarwa a cikin gida. Ya ce ana samun yaɗuwar tsarin CNG a ƙarin jihohi, inda Edo ke da motocin bas 50 masu amfani da CNG da ke aiki, Kano ta sauya sama da motocin kasuwanci 1,000 zuwa CNG tare da faɗaɗa cibiyoyin sauya motoci da tashoshin cike gas.
Ya ƙara da cewa, Delta, Kwara da Legas na faɗaɗa ayyukan sufuri masu amfani da CNG, yayin da Akwa Ibom ta karɓi motocin bas 50 masu amfani da CNG domin fara gudanar da harkokin kasuwanci.
Shugaban ƙasar ya buƙaci kowace jiha ta ci gaba da ƙoƙarin cimma manufar rage farashin sufuri kafin ranar 1 ga Oktoba, tare da yin aiki da ƙungiyoyin ma’aikatan sufuri da masu motocin kasuwanci.
Ya kuma buƙaci jihohin su tallafa wajen sauya motocin zuwa CNG, ƙara yawan motocin da ake amfani da su da kuma samar da abubuwan more rayuwa da ake buƙata. Ya ce babban abin da ya kamata shi ne tabbatar da cewa duk wani tanadin kuɗin da aka samu sakamakon amfani da makamashi mai rahusa ya isa ga ’yan Nijeriya ta hanyar rage musu kuɗin sufuri.
“Nijeriya na da isasshen gas. Muna gina abubuwan more rayuwar da ake buƙata. Tuni muna ganin tanadin kuɗi. Yanzu dole mu ƙara hanzarta tare da faɗaɗa wannan shiri domin ƙarin ’yan Nijeriya su fara jin wannan ragi a kuɗin sufuri da suke biya a kullum,” inji Tinubu.
