Amurka, Denmark da Greenland sun rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniyar tsaro da za ta ba Amurka damar faɗaɗa kasancewar sojojinta a Greenland, bayan watanni ana takaddama kan makomar yankin da ke ƙarƙashin mulkin Denmark.
Shugaban Amurka Donald Trump, Firaministar Denmark Mette Frederiksen da Firaministan Greenland Jens-Frederik Nielsen ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar a gefen taron Majalisar ɗinkin Duniya a New York ranar Talata.
Yarjejeniyar ta tanadi yiwuwar kafa wasu sabbin sansanonin sojin Amurka guda biyu a Greenland, tare da samar da tsarin kariya daga makamai masu linzami da Amurka ta kira “Golden Dome”.
Matakin ya zo ne bayan dogon rikici tsakanin Washington da Copenhagen kan matsayar Trump na cewa Amurka na buƙatar mallaka ko kuma samun cikakken iko kan tsaron Greenland. Yarjejeniyar ta yanzu ba ta mayar da Greenland mallakar Amurka ba, amma ta ƙara rawar da Washington za ta taka wajen tsaron yankin.
Greenland, wadda ke da matsayi mai muhimmanci saboda inda take a yankin Arctic da kuma albarkatun ƙasa da take da su, ta kasance cibiyar fafatawar manyan ƙasashe kan tsaro da tasiri a yankin.
