Trump ya yi barazanar ‘dulmiyar’ da Iran idan ba a cimma yarjejeniya ba

Spread the love

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar cewa kasarsa za ta iya dulmiyewa ko ‘halaka’ gwamnatin Iran idan har ba a cimma yarjejeniyar zaman lafiya ba, a wani jawabi da ya gabatar a gaban taron Majalisar ɗinkin Duniya a birnin New York ranar Talata.

Trump ya ce yana da “babban hukunci” da zai yanke kan ko Amurka za ta cimma yarjejeniya da Iran, ko kuma ta ci gaba da kai mata hare-hare. Ya kuma ce ya yi imanin cewa akwai yiwuwar a cimma matsaya tsakanin Washington da Tehran. 

Ya kuma zargi Iran da jan ƙafa wajen tattaunawar da za ta iya kawo ƙarshen yaƙin, musamman kan sake buɗe mashigar tekun Hormuz, wadda ke da muhimmanci wajen jigilar man fetur a duniya.

Sai dai daga baya, bayan ganawarsa da Firaministan Birtaniya Andy Burnham, Trump ya sauya salo inda ya ce yana ganin ana iya cimma yarjejeniya da Iran, yana mai cewa tattaunawar tsakanin ɓangarorin na ci gaba.

A yayin jawabin nasa, wakilan Iran da ke zauren Majalisar ɗinkin Duniya sun fice daga zauren yayin da Trump ke magana kan hare-haren da Amurka ta kai wa Iran a watannin baya.

By ukarofi

Leave a Reply