Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya ta gurfanar da wasu mata biyu a gaban Kotun Tarayya da ke Legas bisa zargin yaɗa wani saƙon ƙarya cewa Bankin Access zai dakatar da ayyukansa.
Waɗanda ake zargin, Idorenyin Samuel Umobh da Fineness Monday Esu, sun musanta aikata laifin bayan an karanta tuhume-tuhume uku da ake yi musu.
Lauyan da ke wakiltar masu gabatar da ƙara, Stanley Nwafoaku, daga Daraktan Sashen Harkokin Shari’a na Sashen Binciken Laifuka na Tarayya (FCID) na Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya da ke Alagbon, Ikoyi, Legas, ne ya gabatar da matan biyu a gaban kotun.
A cikin ƙarar mai lamba FHC/L/CR/773/2026, masu gabatar da ƙara sun zarge su da “ƙulla makirci tsakaninsu da wasu mutane da har yanzu ba a kama su ba, domin yaɗa wani saƙon ƙarya ta hanyar na’urorin kwamfuta da hanyoyin sadarwa, game da Bankin Access.”
A cewar tuhumar, matan sun yaɗa cewa bankin zai rufe ayyukansa daga ranar 23 ga Satumba 2026, tare da umartar kwastomominsa da su rufe asusunsu kuma su cire kuɗaɗensu, lamarin da masu gabatar da ƙara suka ce an yi shi ne da nufin haifar da tarzoma da karya doka da oda.
An tuhume su da laifin haɗa baki, wanda ake zargin ya saɓa wa Sashe na 27(1)(b) na Dokar Laifukan Intanet ta 2015, wadda aka yi wa gyara a 2024.
A tuhume na biyu, ’yan sanda sun ce Umobh da Esu “da gangan kuma bisa sani” sun aika tare da haddasa yaɗuwar wani saƙo ta kafafen Facebook da WhatsApp, wanda suka san ƙarya ne.
Saƙon ya yi iƙirarin cewa Bankin Access zai dakatar da ayyukan bankinsa daga ranar 23 ga Satumba 2026, tare da kira ga jama’a da kwastomomin bankin da su rufe asusunsu.
Lauyan ’yan sanda ya nemi kotun ta tura matan biyu zuwa gidan yari domin a ci gaba da tsare su, tare da sanya ranar fara shari’ar.
Sai dai lauyarsu, Cyhtia Nwanpu, ta roƙi kotun da ta ba ta ɗan lokaci domin shigar da takardar neman belinsu.
Mai shari’a Akintayo Aluko ya bayar da umarnin ci gaba da tsare waɗanda ake zargin a hannun Hukumar Kula da Gyaran Hali ta Nijeriya (NCoS), sannan ya ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 25 ga Nuwamba 2026.
An ɗage shari’ar ne domin bai wa lauyar kariya damar shigar da takardar neman beli kafin ranar da aka sanya domin ci gaba da shari’ar.
