
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Jihar Kano ta ce ta dakatar da baki ɗaya harkokin da suka shafi hawan dawakai acikin ƙwaryar birnin Kano, tana mai cewa ta yi hakan saboda waɗansu dalilai na tsaro da kuma buƙatar kariya ga yiwuwar fito-na-fito tsakanin jama’a.
An sanar da wannan takunkumi ne a ranar Lahadi bayan wani zaman gaggawa da majalisar tsaron jihar (SSC) ta gudanar a gidan Gwamnatin Kano, inda aka yi nazari akan halin tsaron a game da harkokin da aka shirya.
A cewar sanarwar da Kakakin gwamnatin jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, matakin majalisar na dakatar da hawan dawakan na da nufin ɗaukar matakan kariya ne a yayin tabbatar da biyayya ga doka da oda acikin al’umma da kariya ga rasa rayuka da dukiyoyi.
Gwamnatin ta bayyana cewa, sakamakon binciken tsaro ya nuna cewa akwai wani shiri na tara masu goyon baya da nufin ƙaddamar da wasu hare-hare yayin gudanar da harkokin, lamarin da ya haddasa damuwa kan yiwuwar karya doka da oda.
Akan haka ne kuma gwamnatin ta umarci hukumomin tsaro da su tabbatar da cewa al’umma sun yi biyayya ga dokar da kuma ɗaukar matakan doka akan dukkan wanda aka samu ya karya dokar.
Haka kuma, ta yi gargaɗi akan dukkan wani aiki da zai tayar da zaune-tsaye yayin da al’umma suke halin zaman lafiya, tana mai kira ga mazauna, cibiyoyin gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki da su kwantar da hankali tare da zama masu biyayya ga doka da oda musamman akan umarnin.
