
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A safiyar ranar Lahadi wata mota ta afka cikin ma’ajiyar tukwanan iskar gas a yankin Arab Road da ke Kubwa a babban birnin tarayya Abuja, lamarin da ya haifar da tarwatsewar wasu daga cikinsu da jefa jama’ar wajen cikin firgici.
Al’amarin ya auku ne da misalin ƙarfe 6:15 na safe, wanda shaidu suka ce an ji ƙarar fashewar tukwanan daga nisan kilomita masu yawa daga wajen da abin ya faru.
Mazauna yankin Rukunin Gidajen Ɗantata a Kubwa, wato nisan kilomita biyu daga gurin, sun bayyana cewa hatta gine-ginensu sai da suka amsa bayan fashewar tukwanan. Wannan al’amari ya kuma yi sanadiyyar lalata wani shingen fakewa da allunan alama a Liberty Junction, yayin da gobara ta kama wasu shaguna a kusa da wajen.
An ruwaito cewa, motar da ta yi kutsen ta ƙone ƙurumus, saidai an ceto direban motar da wani yaro da ke ciki tare da garzayawa da su asibiti a nan take.
Tuni dai jami’an kashe gobara da na wasu hukumomin tsaro suka yi ta ƙoƙarin kashe gobarar da dawo da harkoki yadda aka saba a lokacin da suka je wajen.
Haka kuma, an ga yadda mutane suka yi cincirindo a wajen tare da haddasa cinkoso ga zirga-zirgar ababen hawa yayin da jami’an tsaro suka cigaba da ayyukansu.
