NDLEA ta kama ango ɗauke da ƙullin hodar ibilis 72 a filin jirgi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi NDLEA, ta ce ta kama wani sabon ango ɗan shekara 25 kuma ɗan kasuwa a Filin jiragen sama na Akanu Ibiam da ke Enugu bisa zargin sa da yunƙurin safarar ƙulli 72 na hodar ibilis zuwa ƙasar Portugal.

An kama wanda ake zagin ne a babban ɗakin tantance matafiya a ranar Alhamis, 24 ga Satumba, 2026, yayin da yake ƙoƙarin neman gurbi a jirgin Ethiopian Airlines zuwa Portugal ta birnin Addis Ababa.

A cewar NDLEA a wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, wanda ake zargin ya haɗiye baki ɗaya hodar kuma an sanya shi a halin nazari bayan kama shi. Hukumar ta ce daga bisani ya fitar da baki ɗaya ƙunshi 72 ta duburarsa.

Ya shaida wa masu bincike cewa ya kasance mai sana’ar ƙawata mota ne a Trade Fare Complex da ke yankin Ojo a Jihar Legas a baya, kana ya sauya sheƙa zuwa Portugal a watan Mayu, 2023.

A kwanan nan ya dawo Nijeriya kuma ya yi aure a ranar 13 ga Satumba, 2026. NDLEA ta ce, ana zargin ya shiga harkar dillancin ƙwaya ne da nufin warware basussukan da suka taru akansa a lokacin bikin auren nasa.

By Babaji

Leave a Reply