Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
An naɗa Alhaji Abubakar Alolo shugaban kamfanin Mobile Media Crew a matsayin shugaban kwamitin riƙobna Online Media chapel ta ƙungiyar ‘an jarida reshen Jihar Katsina,sai Mustapha Sadiq na kafar Katsina Post a matsayin sakatare da Zaharaddeen Danjuma na Katsina Times a matsayin Ma’ajin ƙungiyar.
Kwamitin riƙon shi zai jagoranci ƙungiyar kafin zaɓe wanda zai kasance na farko bayan ƙaddamar da ƙungiyar.
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya taya Alhaji Abubakar Shafi’i Alolo, shugaban kamfanin Mobile Media Crew, murnar naɗa shi a matsayin shugaban kwamitin riƙo na sabuwar Online Media Chapel ta ƙungiyar ’yan jarida ta ƙasa (NUJ), reshen Jihar Katsina.
Gwamnan ya kuma taya Mustapha Saddiq na kafar Katsina Post, wanda aka naɗa Sakataren kwamitin, da Zaharaddeen Ishaq na jaridar Katsina Times, wanda aka naɗa Ma’aji, murnar naɗinsu cikin kwamitin mai mutum uku.
A cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan, Ibrahim Kaula Mohammed, ya fitar, Gwamna Raɗɗa ya bayyana kafa Online Media Chapel a matsayin muhimmin mataki wajen ƙarfafa ƙwarewa, ɗa’a da haɗin kai tsakanin masu aikin jarida na kafafen intanet a jihar.
Ya ce aikin jarida ta yanar gizo ya zama ɗaya daga cikin manyan hanyoyin da jama’a ke samun bayanai a wannan zamani, lamarin da ke buƙatar ’yan jarida su mayar da hankali kan sahihancin bayanai da ɗaukar alhakin abubuwan da suke wallafawa.
Gwamnan ya buƙaci masu aikin jarida a kafafen intanet su tabbatar da sahihancin bayanai tare da tantance su kafin wallafawa, musamman saboda saurin yaɗuwar bayanai a kafafen sada zumunta.
Ya ƙara da cewa fasahar zamani ta samar da damammaki ga ’yan jarida, amma a lokaci guda ta ƙara musu nauyin tabbatar da cewa bayanan da suke yaɗawa sahihai ne, masu daidaito kuma ba sa nuna son kai.
Gwamna Raɗɗa ya bayyana fatansa na cewa sabuwar Online Media Chapel za ta zama kafar haɗin kai, bunƙasa ƙwarewar aiki da inganta bin ƙa’idojin da’ar aikin jarida tsakanin mambobinta.
Ya kuma jaddada muhimmiyar rawar da kafafen yaɗa labarai ke takawa wajen inganta tattaunawar jama’a cikin lumana, zaman lafiya da ci gaban Jihar Katsina.
Gwamnan ya bayyana ƙwarin gwiwarsa cewa Alolo da sauran mambobin kwamitin za su yi aiki tare da ’yan jarida domin ƙarfafa haɗin kai da gina ingantacciyar Online Media Chapel a jihar.
Ya sake taya Alolo, Mustapha Saddiq da Zaharaddeen Ishaq murnar naɗinsu, tare da yi musu fatan samun nasara a lokacin gudanar da ayyukansu.
