‘Yan ta’adda sun kashe mutum ɗaya a sabon hari a Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Mummunan lamari ya faru a safiyar Lahadi yayin da ‘yan ta’adda suka mamaye yankin Unguwar Sarki dake a garin Bungudu ta jihar Zamfara, inda suka kashe mutum ɗaya sannan suka sace wasu mutum 12.

Wanda aka kashe a lokacin harin an bayyana sunansa da Alhaji Usman Aliyu, wanda aka fi sani da Babangida Kuku.

Majiyoyi a garin sun bayyana cewa waɗanda aka sace sun haɗa da mata huɗu, maza bakwai da jariri ɗaya.

A cewar mazauna garin, ‘yan ta’addan sun mamaye al’ummar yankin da yawa, suka riƙa harbe harbe don sanya tsoro ga alummar yankin kafin su aiwatar da ayyukansu.

Shaidu sun ce maharan sun yi aiki na wani lokaci ba tare da wani ɗaukin gaggawa daga jami’an tsaro ba, lamarin da ya ƙara firgita da tada hankalin mazauna yankin.

“Sun harbe Alhaji Aliyu a nan take, yayin da aka ɗauke mutane 12 zuwa cikin daji”.

Mazauna garin sun yi kira ga hukumomin tsaro da gwamnatin jihar Zamfara da su gaggauta ƙarfafa tsaro a yankin tare da ƙara himma wajen ceto waɗanda aka sace ba tare da wani rauni ba.

A cikin ‘yan watannin nan, ƙaramar hukumar Bungudu ta ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin wuraren da ake yawan samun hare-haren ‘yan fashi, kashe-kashe da garkuwa da mutane a jihar Zamfara, duk da ayyukan soji da ake ci gaba da yi a yankin.

Lokacin da Blueprint Manhaja ta tuntuɓi jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Yazid Abuibakar CC, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa za a sanar da cikakken bayani nan ba da jimawa ba.

By ukarofi

Leave a Reply