Abacha ya ‘yanta mu daga danniya, inji Jonathan yayin cikar Bayelsa shekaru 30

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Ebele Jonathan ya bayyana cewa al’ummar Jihar Bayelsa za su cigaba da kasancewa masu godiya ga marigayi tsohon Shugaban Mulkin Soja, Janar Sani Abacha bisa kafa jihar daga tsohuwar Jihar Ribas a shekarar 1996.

Jonathan, wanda kuma tsohon gwamnan jihar ne, ya bayyana haka ne a ranar Alhamis yayin bikin cikar Jihar Bayelsa shekaru 30 da kafuwa a Yenagoa, a lokacin da yake jaddada jimamin kewar jigo kuma jagoransa na siyasa, marigayi Cif Diepreye Alamieyesigha, wanda ya yi gwamnan jihar daga Mayun 1999 zuwa Disambar 2005.

Jihar Bayelsa ɗaya ce daga cikin jihohi shida da aka kafa a ƙarƙashin gwamnatin Abacha a ranar 1 ga Oktoba, 1996, matakin da ya haɗe kan ‘yan ƙabilar Ijaw waje guda waɗanda a baya suke a rarrabe a tsohuwar Jihar Ribas.

Jonathan, wanda ya yi wa marigayin mataimaki gabanin ya zama gwamna, ya ce ya sadaukar da kyautar karramawar da aka ba shi a taron ga mai gidan nasa, wanda ya bayyana a matsayin wanda ya janyo shi shiga harkar siyasa.

Musamman tsohon shugaban ƙasar ya kuma jinina wa marigayi Janar Abacha kan samar da jihar, inda ya ce al’ummar Bayelsa za su cigaba da yaba wa ƙoƙarinsa akan abin alherin, wanda a cewarsa ba za su taɓa mantawa da shi ba.

Kazalika, ya ce matakin ya taimaka wa jihar wajen amfana da muhimman ababen more rayuwa a ƙarƙashin gwamnatin jiha da ta tarayya, wanda hakan ya yi sanadiyyar inganta al’ummarsu a shiyyar Kudu da ma ƙasa baki ɗaya.

By Babaji

Leave a Reply