Tinubu ya ceci Nijeriya daga ɗaiɗaicewa, inji Shettima

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, ya ce muhimman matakan tattalin Shugaba Bola Tinubu sun ceci Nijeriya daga rushewar tattalin arziƙi da kuma kare ƙasar daga ɗaiɗaicewa. Shettima ya bayyana haka ne a yayin ganawa da ‘yan jarida a ranar Asabar jim-kaɗan bayan kai wa Shugaba Tinubu ziyara a Legas.

Da yake bayar da kariya ga matakan tattalin arziƙi da gwamnatinsu take ɗauka, Shettima ya ce a lokacin da suka kama aiki sun samu ƙasa da Dala biliyan 3.9 na rarar kuɗaɗen Nijeriya a asusun ƙasashen waje, yana mai bayyana tattalin lokacin a matsayin abin da ke kan gaɓar rugujewa, kamar yadda aka ruwaito a Venezuela, wanda a cewarsa, bai kai kuɗin shigo da fetur ba na wata guda.

Ya ce, Tinubu ya kwaɗaitar da “ƙwarin-gwiwa da aiwatarwa” wajen ɗaukar matakan cire tallafin fetur da sake daidaita matakin canjin kuɗaɗen waje domin ciyar da Nijeriya gaba ta fuskar tattali domin amfanin al’umma da ma ƙasar baki ɗaya.

Ya bayyana cewa, yayin halin matsin tattali da al’ummar ƙasa suka tsinci kansu a ciki, gwamnatin tana aiwatar da shirye-shirye da ayyuka da manufar rage wahalhalu akan ‘yan ƙasa. “Muna sane da raɗaɗin da ‘yan Nijeriya suke fuskanta, amma halin matsi ba ya ɗorewa; mutane masu jajircewa suna ƙoƙarin shawo kansa,” inji Shettima.

A cewarsa, gwamnatin a ‘yan makonnin da ke tafe za ta ƙaddamar da wasu shirye-shirye, ciki har da samar da tsarin aiken kaya na zamani a Arewa maso Yamma da adaidaita sahu masu amfani da lantarki a Arewa maso Gabas guda 10,600 da kuma motocin bos guda 300 da ƙananan motocin sufuri masu amfani da lantarki, yana mai cewa hakan na da nufin rage raɗaɗin matsin tattalin da al’umma suke fuskanta a sassan ƙasar.

By Babaji

Leave a Reply